Gwamnonin Arewa Sun Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Gwamna Zulum.

Gwamnonin Arewa Sun Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Gwamna Zulum.

kungiyar Gwamnonin Arewa ta yi tir da Allah wadai kan harin da aka kai wa Gwamna Babagana Zulum na Borno ranar Laraba, inda ta bayyana harin a matsayin ta’addanci ƙarara.

Shugaban kungiyar kuma Gwamnan Filato, Simon Lalong, ne yayi Allah wadai din cikin sakon da Daraktan watsa labaransa, Dakta Makut Macham ya bayyana.

Ya ce harin da aka kai wa Gwamnan a kan hanyarsa ta Baga cikin karamar hukumar Kukawa ta jihar wani aiki ne na kokarin hana shi taimaka wa raunanan al’ummar jihar.

Gwamnan ya nuna damuwarsa ganin cewa an kai wa Zulum hari ne lokacin da yake kan hanyarsa ta kai wa ‘yan gudun hijira kayan hidimar Sallah.

Yadda ƴan Boko Haram suka yi yunƙurin halaka gwamnan Borno
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/boko-haram-sun-kai-was-umara-zulum-hari.html?m=1

Lalong ya ce harin wani aiki ne daga wasu baragurbin da suke kokarin hana gwamnan rage wa ‘yan gudun hijira radadin da ‘yan ta’adda suka jefasu a ciki wani yanayi.

Wannan harin ya nuna ƙarara akwai makiya zaman lafiya da mutane da basa jin dadin rage wa jama’a wahala da Gwamnan madugu uban aiki yake.

kungiyar Gwamnonin Arewa cikin kakkausar murya na Allah wadai da wannan harin, kuma tana goyon bayan Gwamna Zulum wanda ya nuna kwazo wajen kai wa mutane tallafi ko da yana cikin hatsari.

Muna kira gare shi da kada ya taba tsorata yayin da yake aiki tare da jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar, inji shi.

Gwamna Zulum ya caccaki Sojoji kan Harin Baga 
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/gwamnan-zulum-ya-caccaki-sojoji-bayan.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.