Muna cikin tashin hankali a Borno – Shehun Borno

Muna cikin tashin hankali a Borno – Shehun Borno

Mai Alfarma Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi ya koka yadda shugabanni da mazauna Jihar Borno ba su tsira ba daga hare-haren ƴan bindiga.

Basaraken yana magana ne kan harin da aka kai wa tawagar Gwamna Babagana Umara Zulum yayin da yakai wa Gwamnan ziyarar Sallah a fadar gwamnati da ke birnin Maiduguri.

A ranar Laraba ne aka kai wa jerin motocin gwamnan hari a garin Baga na Ƙaramar Hukumar Kukawa lokacin da yake kan ziyara a yankin.

Gwamnan Zulum ya caccaki Sojoji kan Harin Baga 
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/gwamnan-zulum-ya-caccaki-sojoji-bayan.html

An ga Gwamna Zulum a wani bidiyo lokacin da harin ke faruwa yana zargin sojojin da gazawa sannan daga baya ya zarge su da yi masa zagon ƙasa.

“Idan har za a kai wa babban mutum irin wannan hari, Wanda yake Shugaban tsa a jiha, to ina tabbatar muku cewa babu wanda ya tsira a jihar nan,” inji Shuehun Borno, kamar yadda mai bai wa gwamna shawara kan kafofin yaɗa labarai Isa Gusau ya rawaito.

Ya ci gaba da cewa: “Mai girma gwamna ba muji daɗin abin da ya faru ba a Baga, kuma abin tausayi ne. Yanayin ƙara munana yake.”

Elkanemi ya nemi jama’a da su ci gaba da addu’a domin kawo ƙarshen matsalar Boko Haram, wadda ta janwo asarar rayukan mutum fiye da 20,000 a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya

Zulum ya kai wa ƴan gudun hijira 80,000 tallafi a Monguno
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/zulum-ya-kai-wa-gudun-hijira-80000.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.