Trump zai Rufe TikTok a Amurka

Trump zai Rufe TikTok a Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai haramta amfani da manhajar dandalin TikTok a ƙasarsa.

Ya faɗa wa manema labarai cewa zai saka hannu kan wata dokar ɓangaren zartarwa nan da ranar Asabar.

Jami’an tsaron Amurka sun bayyana fargabvar cewa za a iya amfani da manhajar, wadda kamfanin ByteDance na China ya mallaka, wurin satar bayanan Amurkawa.

TikTok ya ƙaryata zargin cewa gwamnatin China ce ke iko da shi kuma ba ya bai wa gwamnatin bayanan masu amfani da shi.

Dandalin wanda ake ɗauka tare da yaɗa gajeriun bidiyo, na da masu amfani da shi miliyan 80 duk wata a Amurka kuma rufe shi ba ƙaramar asara ba ce ga kamfanin.

“Game da TikTok, za mu toshe shi a Amurka,” in ji Trump, yayin da yake magana a jirgin sama.

Leave a Reply

Your email address will not be published.