Buhari yana ganawa da hafsoshin tsaro a fadarsa

Buhari yana ganawa da hafsoshin tsaro a fadarsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana jagorantar taro kan sha’anin tsaro a fadarsa da ke Abuja, babbarn birnin kasar, a cewar mai taimaka masa kan shafuan zumunta.

Sakon da Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce hafsoshin tsaron kasar da sauran manyan masu ruwa da tsaki kan tsaro a gwamnatinsa na cikin mahalarta taron.


Sai dai bai yi karin bayani kan abubuwan da suke tattaunawa ba.

Ana wannan taro ne kwanakin kadan bayan gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya zargi jami’an tsatron kasar da yin zagon ƙasa a yunkurin magance matsalar Boko Haram.

GWAMNA ZULUM YA TONA ASIRIN WAƊANDA SUKE CIN AMANA A YAƙI DA TA’ADDANCIN BOKO HARAM
https://www.arewagist.com.ng/2020/08/gwamna-zulum-ya-tona-asirin-waanda-suke.html?m=1

Leave a Reply

Your email address will not be published.