GWAMNA ZULUM YA TONA ASIRIN WAƊANDA SUKE CIN AMANA A YAƙI DA TA’ADDANCIN BOKO HARAM

GWAMNA ZULUM YA TONA ASIRIN WAƊANDA SUKE CIN AMANA A YAƙI DA TA’ADDANCIN BOKO HARAM

Wannan jawabi na tonon asiri BBC Hausa suka ruwaito cewa Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum yace jami’an tsaro na yin zagon ƙasa a yunƙurin kawar da ƙungiyar Boko Haram.

Wato turace ta kai bango, Gwamna Zulum yace bai zai iya yin shiru ba ana ci gaba da kashe al’ummarsa da sunan ta’addancin Boko Haram saboda rantsuwar da yayi da Al-Qur’ani tsakaninsa da Allah cewa zai kare rayuka da dukiyoyin jama’ar Borno.

Zulum ya yi wannan jawabin ne a lokacin da wasu gwamnonin Arewa suka kai masa ziyarar jaje bayan harin kwanton ɓauna da ‘yan Boko Haram ko wasu maciya amanar tsaron Nigeria suka ƙaddamar masa a garin Baga da nufin hallakashi.

Farfesa Babagana Umara Zulum yace akwai bukatar Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya san cewa cin amana da zagon kasar da ake yi a yaƙi da ta’addancin Boko Haram shine ya kawo cikas wajen kawo karshen ta’addancin Boko Haram daga doron duniya.

Gwamnan yaci gaba da cewa: “ba na neman wa’adi na biyu, idan Allah Ya nufe ni da kammala wannan wa’adi na farko to Alhamdulillah, amma ni a matsayina na gwamna, nayi shiru al’umma jihar Borno miliyan shida su mutu, su ƙare, hakan ba zai zama alheri gare ni ba.

 Na yi rantsuwa tsakanina da Allah zan kasance mai gaskiya ga al’ummata,” in ji Gwamna Zulum

Gwamna Zulum ya kuma tuhumi abin da ya sa sojojin Nigeria suka hana dubban mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu komawa garuruwa da gidajensu, saboda su sojojin ne ke noma a filayen mutanen, shiyasa basa son mutanen su koma

BBC ta tuntuɓi rundunar sojin Nigeria don jin martaninta game da waɗannan manyan zarge-zarge, amma rundinar sojin ta ce ba ta sa-in-sa da shugabannin siyasa.

 Sojoji ba za su ce uffan kan zarge-zargen Gwamna Zulum ba, saboda su ba sa musayar yawu da shugabannin siyasa

Leave a Reply

Your email address will not be published.