Wani bam ya tashi a Beirut na Lebanon

Wani bam ya tashi a Beirut na Lebanon

Wani bam ya tarwastse a babban birnin Lebanon, Beirut yayin da ake jiran yanke hukunci kan kisan tsohon firaministan ƙasar Rafik Hariri a shekarar 2005.

Rahotanni sun ce fashewar ta faru ne a kusa da tashar jirgin ruwa da ke birnin, sannan wasu rahotannin suka ce an ji ƙara ta biyu.

Mahukunta na fargabar cewa waɗanda suka ji rauni na da yawa.

Wani bidiyo da aka wallafa a intanet ya nuna wani baƙin hayaƙi ya turnuƙe sama sannan kuma ya yi ɓarna.

Wata kotun Majalisar Ɗinkiin Duniyta ce ke shirin bayar da hukunci game da shari’ar, wadda ake zargin mutum huɗu bayan an aikata kisan ta hanyar tashin wani bam a mota.

Leave a Reply

Your email address will not be published.