Buhari ya baiwa hafsoshin tsaro umarnin sabunta dabarun yaƙar ta’addanci

Buhari ya baiwa hafsoshin tsaro umarnin sabunta dabarun yaƙar ta’addanci

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ɗibarwa shugabannin rundunonin tsaron Najeriya wa’adi na su sake jan ɗamara tare da sabunta hanyoyin yaƙi da ‘yan ta’addan da suka addabi kasar.

Buhari ya gargadi hafsoshin tsaron da cewar gaza shawo kan matsalar, zai sa shi daukar mataki tsattsaura ganin yadda sha’anin tsaro a Najeriya ke ci gaba da taɓarɓarewa.


Mai bawa Shugaba Buhari shawara Kan Harkar tsaro Baba Gana monguno ya ce Yawaitar ƙwayoyi Masu sa maye ne ummul aba isin Wannan matsala.

Sannan ya ce Shugaban Buhari ya faɗa musu su sake Shirin yaƙi da ta’adanci, idan ba haka ba, Akwai abinda zai biyo baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.