Buhari ya tsawaita dokar kulle na tsawon sati huɗu

Buhari ya tsawaita dokar kulle na tsawon sati huɗu


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake tsawaita dokar kullen da aka sassauta kashi na biyu na tsawon makonni huɗu.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa na yaƙi da cutar korona Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani bayani ga ‘yan jarida kan cutar.

ƙwamitin Kar ta kwana Bai buƙaci Sai anyi wa ɗalibai gwajin Korona ba kafin su koma makaranta, inji Coordinator na ƙasa Dakta Sani Aliyu

Wannan ne dai karo na uku da aka tsawaita kashi na biyu na sassaucin dokar kullen a faɗin ƙasar.

Akwai shawarwari da sakataren gwamnatin ya bai wa shugaban ƙasar kan ci gaba da sassaucin wannan doka, sai dai ba a fito da bayanai kan shawarwarin ba.

ISIS da Al-Qaeda ‘sun kutsa yankin arewa maso yammacin Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published.