Sabuwar kungiyar mayaƙan ta’addanci ta bayyana a Kamaru

Wata sabuwar ƙungiyar ƴan tawaye ta ɓulla a Kamaru


Wata sabuwar kungiyar ƴan tawaye ta kunno kai a Kamaru, sai dai ƙungiyar ba ta bayyana sunanta ba. Ƙungiyar ta fara ne da watsa wani bidiyonta na farko a shafukan sada zumunta, wanda yanzu haka suka karaɗe kasar ta Kamaru.

Cikin bidiyon, ɗaukacin dakarunta da aka hasko na sanye da kayan yaƙi kamar yadda sojojin gwamnati suke yi kuma suna ɗauke da makamai.

Manufar wannan ƙungiyar da ta bayyana a cikin bidiyon ita ce karɓe mulki daga hannun shugaban ƙasa Paul Biya, wanda ya daɗe yana shugabantar Kamaru, kamar yadda wani mutum ya bayyana da faransanci a cikin bidiyon.

Cikin bidiyon dai, wani babba daga cikin ‘yan tawayen ya ci gaba da bayani da Fulatanci irin na ‘yan ƙabilar Umbororo ‘yan asalin ƙasar waɗanda ake samun irinsu a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika.

BBC ta nemi karin bayani daga kakakin ma’aikatar tsaro ta ƙasar, sai kakakin ma’aikatar tsaro ya ce bidiyon na bogi ne kuma bai kamata a mayar da hankali a kan shi ba. 

Kamaru ta shafe shekaru tana fama da rikicin ƙungiyoyin ‘yan tada ƙayar baya irinsu Boko Haram da masu fafutukar Ambazoniya masu rajin kafa kasa, kuma har ya zuwa yanzu ƙasar ana fafatawa da ƙungiyoyin.

ISIS da Al-Qaeda ‘sun kutsa yankin arewa maso yammacin Najeriya 

Leave a Reply

Your email address will not be published.