Amurka ta damu game da taɓaɓarewar siyasar Jihar Edo

 

Amurka ta damu game da taɓaɓarewar  siyasar Jihar Edo

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya bayyana damuwa game da “taɓaɓarewar siyasar Jihar Edo”, wadda hukumar INEC ke shirin gudanar da zaɓen gwamna a watan Satumba.

“Amurka ba ta ji daɗin abubuwan da ƴan siyasa (a Edo) ke aikatawa ba,” a cewar wata sanarwa da ofishin ya wallafa a shainfsa na Twitter ranar Juma’a.

Sanarwar ta ƙara da cewa Amurka za ta tallafa wa Najeriya wurin tabbatuwar dimokuraɗiyya “matuƙar dai za a riƙa bai wa talakawan Najeriya waɗanda suka zaɓa”.

Gwamnan Edo ya ƙwaye Rufin Majalisar Dokokin Edo

https://www.arewagist.com.ng/2020/08/obaseki-ya-cire-rufin-majalisar-dokokin.html

Jijiyoyin wuya sun fara tashi a Jihar Edo da ke Kudu maso Kudancin Najeriya ne bayan rantsar da mambobin majalisar dokokin jihar su 14, waɗanda suka yi yunƙurin karɓe ikon majalisar.

A watan Satumba mai zuwa ne za a gudanar da zaɓen gwamna a jihohin Edo da kuma Ondo.

Amurka ta ce tana kallon Najeriya a matsayin “uwa a Afirka” sannan ta yi kira ga masu ruwa da tsaki ciki har da hukumar zaɓe da su tabbata an yi zaɓen adalci kuma mai cike da zaman lafiya

Leave a Reply

Your email address will not be published.