Ya kamata mulki ya koma yankin Kudu suyi shekara taƙwas -El Rufa’i

 

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya ce kamata ya yi mulki ya koma yankin Kudanci idan Shugaba Buhari ya kammala wa’adinsa a 2023.

A hira da yayi da Sashen Hausa na BBC, El-Rufai ya ce duk da dai ba a rubuce tsarin na karɓa-karɓar da ake amfani da shi a siyasance yake ba, yana da kyau a mutunta shi tun da kowane ɓangare ya yi na’am da shi.

“Akwai tsarin da ake bi na karɓa-karɓa, inda kowa ya amince cewa idan Arewa ta yi mulki shekara takwas, Kudu zai yi mulki shekara takwas”, inji El-Rufai.

Ya kara da cewa, “Shi yasa na fito nace bayan Shugaba Buhari ya yi shekara takwas, kada wani dan Arewa ya nemi mukamin. A bar ‘yan kudu suma su samu shekara takwas”.

To sai dai saɓanin yadda ake ta hasashe, gwamnan ya ce sam ba shi da sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Ya ce, “Allah Shi Yake ba da mulki, ko kana so ko ba ka so idan yana so zai ba ka amma ni ban taba neman shugabancin Najeriya ba, ba wanda zai ce na taba nema,” inji gwamnan.

An dade ana harsashen yiwuwar tsayawarsa takarar idan Buhari ya kammala wa’adinsa, yayin da wasu kuma suke kira da cewa lokaci ya yi da kasar za tayi watsi da tsarin na karba-karba ta koma zaben cancanta.

Ko a kwanakin nan, kiran da wani makusancin Shugaba Buhari, Mamman Daura yayi cewa lokaci ya yi na jingine yanki a bi cancanta wajen zaben magajin Buharin a 2023 ya tayar da kura.

Leave a Reply

Your email address will not be published.