Yan Sanda Sun Kashe ƴan Bindiga 8 tare da kuɓutar da shanu 30

 

Yan Sanda Sun Kashe ƴan Bindiga 8 tare da kuɓutar da shanu 30

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ce ta kashe wasu mutane 8 da ake zargi da yin garkuwa da mutane da kuma gano shanu 30 sakamakon wani sumame a wani kauye na Zamfarawa a karamar Hukumar Batsari.

Kakakin  rundunar, SP Gambo Isah, ya ce: “A ranar 06/08/2020 da misalin 01: 00hrs, DPO Batsari Division ya jagoranci” Operation Puff Adder “da” Sharan Daji “zuwa ƙauyen Zamfarawa Batsari na jihar Katsina dangane da bayar da rahoton cewa ƴan fashi arba’in (40), ɗauke da bindigogi kirar AK 47, suna harbi ba kakkautawa, suka kai hari ƙauyen, suka kashe Shafi’i Suleiman, M, mai shekaru 65 da Yakubu Idris, M, mai shekara 70yrs kuma suka kwace adadin shanu da ba a bayyana yawansu ba. .

yan bindigar sun kai wa ƴan sandan kwantan ɓauna a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa kauyen.

“A sakamakon haka, Jami’an tsaron suka maida wuta kuma nan take suka kashe ɗaya daga cikin maharan yayin da wasu suka tsere zuwa cikin daji tare da raunukan harsasai.

Rundunar ta yi nasarar gano shanu 30 da ɓarayin suka sace daga kauyen.

Ya kara da cewa, “Bayan haka, a ranar 7/08/2020, ɓangarorin masu bincike na sirri karkashin jagorancin DPO suka gano karin gawarwaki bakwai na ‘yan bindiga a kauyen Barankada, Batsari ta jihar Katsina,”

Ya ce an samu kwatankwacin N22, 300, harsasai guda goma sha uku da kuma albarusai biyu na 7.62mm, makulli da sauransu da aka gano ajikin gawarwakin da abin ya faru dasu daidai lokacin da ake binciken.

Leave a Reply

Your email address will not be published.