Ba za a bude kasuwannin Kaduna ba sai an samu lafawar yaduwar Korona a jihar – El-Rufai


Ba za a bude kasuwannin Kaduna ba sai an samu lafawar yaduwar Korona a jihar – El-Rufai


Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa, ba zai bude kasuwannin Kaduna ba saboda yadda ake fama da cigaba da yaduwar Korona a jihar.


El-Rufai ya bayyana haka a tattaunawar sa da BBC Hausa.


Su ƴan kasuwa suna cewa sun fara bara. Mun ji, amma gara kayi bara kana da rai da ka mutu.


Gwamna El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta buɗe kasuwanni da wuraren ibada ne kawai bayan jihar ta iya dakile yaduwar Korona ta yadda ba a samun wadanda suke kamuwa da yawa.


“Bayan rufe jiha da muka yi kwana 75, sannu a hankali mun buɗe wasu sassan na rayuwa domin muga ko mutane za su yi biyayya ga dokokin da jami’an kiwon lafiya suka gindaya domin kare al’umma daga kamuwa da cutar ta korona.”


Sai dai kuma ya koka da yadda mutane a jihar ba sa kiyaye dokar Korona musamman wajen cuɗanya da mutane da kuma wasu dokokin kariya.


“Idan muka buɗe masallatai da kasuwanni, cunkoson da muke gani ana yi zai karu matuka don ba raguwa zai yi ba. Kuma mutum ɗaya da ke da cutar na iya yaɗa ta ga dubban mutane.”


Ya kuma ce saboda yadda cutar ke kara yaduwa a jihar, gwamnati na iya daukar wasu mataikai.


” Yanzu ma abin da muke dubawa shi ne, ƙila mu rufe jihar domin yadda cutar ke ƙaruwa. Muna fargabar yana iya fin ƙarfin asibitocinmu. Ƙila mu sake rufe jihar a koma gidan jiya.”


Sai dai kuma a karshe ya bayyana cewa gwamnati za ta tallafa wa ƴan kasuwa, idan komai ya koma dai-dai


“Za mu sami hanyoyin tallafa mu su bayan komai ya lafa, amma mutumin da ya riga ya mutu, ko wace irin kasuwanci yake yi ba zai amfane shi ba, sai dai ta lahira.”


Leave a Reply

Your email address will not be published.