Gwamnatin Burtaniya ta Hana mutanan ta zuwa wasu jihohin Najeriya

A hana Turawan Birtaniya tafiya arewacin Najeriya

Gwamnatin Birtaniya ta shawarci al’ummarta da ke zaune a Najeriya da su ƙaurace wa tafiye-tafiye zuwa wasu jihohin arewaci da kudancin kasar saboda taɓarɓarewar matsalar tsaro.

Jihohin sun hada da Borno da Yobe da Adamawa da Gombe da Kaduna da Kano da Bauchi da Niger da Jigawa da Katsina da Zamfara da Kogi da Abia da kuma Rivers.


Sauran jihohin sun hada da Delta da Bayelsa da Akwa Ibom da kuma Cross River.


Sanarwar da Birtaniya ta fitar a shafin ofishinta mai kula da lamurran kasashen ƙetare ta ce, matsalar tsaro ce ta tilasta ɗaukar matakin wucin gadi na janye wani adadi na ma’aikatanta da ke Ofishin Jakadancinta na Abuja da kuma karamin Ofishin Jakadancinta da ke birnin Lagos.


Kodayake ofisoshin biyu na ci gaba da gudanar da muhimman ayyuka da suka hada da taimaka wa Turawan Birtaniya da ke zaune a Najeriya.


A bangare guda, Birtaniyar ta ce, kungiyoyin ƴan ta’adda masu nasaba da Al Qaeda na gudanar da aikinsu a jihar Kaduna kamar yadda ta samu rahotanni a cewarta.


Jihohin arewacin Najeriya musamman Borno da Yobe na fama da rikicin Boko Haram, yayin da ‘yan bindiga suka addabi Zamfara da Katsina da kuma Kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published.