Biafra: IPOB da Ohaneze Ndigbo na shirin dunkulewa

 

Biafra: IPOB da Ohaneze Ndigbo na shirin dunkulewa

Manyan kungiyoyi biyu na ‘yan kabilar Ibo da ke kudancin Najeriya sun soma tattaunawa da nufin dunkulewa waje guda domin tattabar da sun cimma burinsu.

Kungiyar IPOB mai kokarin ballewa daga Najeriya domin kafa kasar Biafara da kuma kungiyar Ohaneze sun tabbatar wa da sashin Ibo na BBC cewa a yanzu sun dinke barakar da ke tsakaninsu.

Kuma sun jaddada cewa duk da suna da bambanci a manufofinsu amma dai zai yi aiki tare domin ciyar da al’ummar Ibo gaba.

Lauyan ‘yan IPOB Aloy Ejimako da kuma daya daga cikin shugabannin kungiyar Ohaneze, Damian Okeke-Ogene sun shaida BBC cewa za su ci gabada tattaunawa a tsakaninsu domin cimma matsaya kan batutuwa da dama a nan gaba.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kungiyoyi biyu na aiki tare ne domin fitar da dan takarar shugaban kasa daga kabilar Ibo a zaben shugaban kasa na shekara ta 2023 a Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published.