Gwamnatin Najeriya ta roki manyan kasashe su daina ƙin siyar mata makaman yaƙi

Gwamnatin Najeriya ta roki manyan kasashe su daina ƙin siyar mata  makaman yaƙi da ta’addanciGwamnatin Tarayya ta roki manyan kasashen duniya suyi watsi da bayanan soki-burutsu ko tsayawa tankiya da gardama, suna hana Najeriya makaman da za suyi yaƙi da Boko Haram.

Ministan Yaɗa Labarai, Lai Mohammed ne ya bayyana haka a wata tattaunawa ta musammam da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) suka yi da shi, ranar Alhamis a Abuja.

“Ina so nayi amfani da wannan dama na bayyana cewa manyan kasashen duniya da su kara kaimin taimakon da suke yi mana, fiye da wanda suke yi a yanzu.

“Shi yaki sai da makami. Don haka idan har muna son yin galaba kan Boko Haram, to fa sai da manyan makamai.

“Matsawar manyan kasashen duniya za su bi ruɗin wasu tashar watsa labarai, masu ɓatanci kan Najeriya su kafa hujja da su, su rika hana mu makamai, to a daina korafin cewa Najeriya ta gaza wajen daƙile Boko Haram.

Lai ya ce akwai wasu kasashen duniya da hatta makamai wadanda za muyi yaƙi da su, duk sun daina siyar mana suka yi.”

 Ministan bai ambaci sunayaen kasashen ba, ya dai kara da cewa, “mun biya kudin makamai da kayan gyaran makamai, an ki kawo mana kayan yaki, an ki ba mu kudin mu. Sannan kuma ko kayan gyara ma ba su raba mana ba.

“Ni kiran da zan yi wa wadannan kasashe shi ne su dubi kalubalen da ke gaban Najeriya, ta bamu makamai domin mu samu mu ragargaji ‘yan ta’adda..

Lai ya yi korafin cewa ‘yan Najeriya ba su gani, kuma ba su jinjina wa Shugaba Muhammadu Buhari kan kokarin sa na shawo kan kashe-kashen ta’addanci.

Ya ce ya kamata a rika auna irin tabarbarewar tsaro tun daga 2015, to za a iya fahimta kan irin ci gaba da gwamnatin Buhari ta samu a yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.