An gurfanar da mahaifin yaron da aka ɗaure a turken dabbobi

An gurfanar da mahaifin yaron da aka ɗaure a turken dabbobi

Rundunar ƴan sanda a jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya ta bayyana cewa ta gurfanar da mahaifin yaron nan da aka ɗaure a turken dabbobi a gaban kuliya, bayan ta kammala bincike da take yi a kan lamarin.

Rundunar na tuhumarsa ne da tauye haƙƙin yaron, sakamakon gazawar mahaifin wajen sauke wajibinsa na kula da ɗan da ya haifa.

A karshen makon jiya ne jami`an wata ƙungiyar farar hula suka bankaɗo inda aka ɗaure yaron, wanda daga nan ƴan sanda da gwamnatin jihar Kebbi suka shiga cikin maganar.

DSP Nafi`u Abubakar kakakin rundunar ƴan sanda, ya shaida wa BBC cewa mahaifin ya tabbatar masu da cewa an haifi yaron ne da wata rashin lafiyar taɓin hankali saboda ya gaji da neman magani ne ya ɗaure shi don ya hana shi fita.

Yadda za ka Sami tallafin da gwamnatin tarayya za ta bayar na Naira Bilyan 75 
https://www.arewagist.com.ng/2020/08/yadda-za-ka-sami-tallafin-da-gwamnatin.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.