An samu karuwar yawan marasa ayyukan yi a Najeriya

An sami ƙaruwar yawan marasa ayyukan yi a Najeriya

Hukumar ƙididdiga a Najeriya ta ce adadin rashin aikin ya kai kashe 27.1 a alƙalumman farko da ta fitar tun 2018.

Adadin ya ƙaru ne daga 23.1 na rashin aikin yi da aka fitar a 2018 zuwa 27.1 a 2020.

Hukumar ta ce sama da kashi ɗaya bisa huɗu na ma’aikata sun rasa ayyukan yi a 2020. Kuma yawan adadin matasa da suka rasa ayyukan yi tsakanin ƴan shekara 15 zuwa 34 ya kai kashi 34.1 wanda shi ne adadi mafi girma.

Annobar korona ta kara haifar da taɓarbarewar tattalin arziki a Najeriya bayan faduwar farashin danyen mai da cutar ta haifar.

Yadda za ka Sami tallafin da gwamnatin tarayya za ta bayar na Naira Bilyan 75 
https://www.arewagist.com.ng/2020/08/yadda-za-ka-sami-tallafin-da-gwamnatin.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.