Banking CBN ya fitar da yadda za ka Kare Asusunka daga ɓarayin INTERNERT

Banking CBN ya fitar da yadda za ka Kare Asusunka daga ɓarayin INTERNERT

Duk sanda tsautsayi ya sa ka jefar da wayar ka, ko ka haɗu da ɓata gari suka ƙwace maka wayar ka, in har kasan kayi rijistar asusun Banki da layin dake cikin wayar.

Ko kuma ka haɗu da ƴan yahoo suka fara zarar maka kuɗi daga Banki.

Hanzarta ka nemi wata wayar da ke kusa, ko ta waye idan har akwai layin waya me aiki a ciki.

Kawai ka danna wannan lambobin *966*911#  a wayar ko wace iri ce, kuma ko wanne irin layi ne acikin wayar,

zaka ga ya nuna ma inda zaka saka “Lambar asusun ka na banki (Account Number)”

Sai ka danna ‘Ok’ ko ‘Send’ take banki zasu tsaida duk wata hanya da za’a iya cire kuɗi a asusun ka musanman (katin ATM).

Yadda za ka Sami tallafin da gwamnatin tarayya za ta bayar na Naira Bilyan 75 

Leave a Reply

Your email address will not be published.