Yan Sanda Sun Kashe ƴan Bindiga Da ƙwato Babura A Katsina

Yan Sanda Sun Kashe ƴan Bindiga Da ƙwato Babura A Katsina

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta ce ta yi nasarar bindige ‘yan ta’adda guda biyu tare da kwato mutun biyu da aka yi garkuwa da su, sannan ta kama babura guda bakwai wadanda ‘yan bindigar ke amfani da su wajan kai hare-hare.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isah ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Katsina inda ya kara da cewa wannan nasara ta samun ne a karkashin ‘operation Puff Adder’

A cewar SP Gambo Isah a shekaran jiya Laraba jami’ansu suka samu rahotan sirri karkashin ‘operation Puff Adder’ cewa ‘yan bindiga dauke da bindigogi kirar AK47 sun kai hari a wani kauye Kwaro da ke cikin karamar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina

“A wannan hari da suka kai sun kashe mutun daya mai suna Mohammed Auwal tare da yin garkuwa da mutane biyu domin neman kudin fansa, sannan sun kwashe dabbobin da har yanzu ba a kai ga tabbatar da adadin su ba” inji sanarwar.

Haka kuma sanarwar ta kara da cewa da jin wancan labari jami’ansu ba su yi wata-wata ba a karkashin aikin na musamman na ‘operation Puff Adder’ suka yi wa ‘yan ta’adda nan kwanton ɓauna, inda suka yi nasarar halaka mutun biyu sauran suka ari na kare cikin dajin sannan suka bar baburansu har guda bakwai

SP Gambo Isah ya cigaba da bayanin cewa mutanen da jami’ansu suka yi nasarar kwatowa daga hannun ‘yan ta’adda sun hada da Musa Rabi’u da Rabi’u Sani, haka kuma sun sami gidan alburushi na AK47.

Kazalika ya kara da cewa da yawan wadannan ‘yan bindiga sun tsere da raunuka a jikinsu wanda yanzu haka ana cigaba da farautarsu a cikin da jin, kuma akwai yiwuwar a kama su ko kuma a samu gawawakinsu.

Kakakin Rundunar ya bayyana cewa yanzu haka sun fara bincike kan wannan lamari kuma da zaran sun kammala sa zu sanar da al’umma halin da ake ciki sannan su dauki mataki na gaba

Leave a Reply

Your email address will not be published.