Shirin N-Power ya azurta mutum 109,823 – Ministar Agaji

Shirin N-Power ya azurta mutum 109,823 – Sadiya Umar

Sadiya Umar Farouq, Ministar Ma’aikatar Agaji da Cigaban Al’umma a Najeriya, ta ce shirin N-Power ya azurta matasan da suka ci gajiyar shirin ta hanyar mayar da mutum 109,823 ‘yan kasuwa.

Ministar ta bayyana hakan a ranar ƙarshe taron da aka shirya na cika shekara guda da kafa ma’aikatar tata.

“Ya zuwa ƙididdigarmu ta ƙarshe, matasa kusan 109,823 na Rukunin A da B sun kafa harkokin kasuwanci a unguwanninsu, abin da ke nuna alfanon shirin na N-Power,” in ji ta.

Ta ci gaba da cewa: “Mun samu nasarar cire mutum 500,000 na Rukun A da B (daga shirin) sannan mun rufe karɓar rajistar Rukunin C, inda mutum 5,042,001 suka nema.

“Yayin da muke ƙoƙarin fara tantancewa, ma’aikatarmu za ta tabbatar cewa an yi adalci don ganin cewa waɗanda suka cancanta kawai za a ɗauka.”

A ranar 21 ga watan Agustan 2019 aka rantsar da Sadiya Umar Farouq a matsayin ministar kula da Ayyukan Jinkai da Kare Afkuwar Bala’i da Cigaban Al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published.