Gwamna Zulum ya ƙona tan 20 na miyagun ƙwayoyi a Borno

Gwamna Zulum ya ƙona tan 20 na miyagun ƙwayoyi a Borno

Gwamnan Jihar Borno Baba gana Umara Zulum ya jagoranci jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ƙona wasu ƙwayoyin magani da hukumar ta kama a ranar Juma’a.

Yayin taron wanda shugaban hukumar ta NDLEA, Kanar Mustapha Abdallah ya shirya, an ƙona tan 20 ko kuma kilogiram 20,000 na ƙwayoyin da hukumar ta kama a sumame daban-daban.

Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ta ce bikin ya gudana ne a Muna da ke kan hanyar Maiduguri-Gamboru ta Jihar Borno.

Cikin manyan baƙin da suka halarci bikin har da Mai Alfarma Shehun Borno – wanda aka wakilta – da manyan jami’an rundunar sojojin Najeriya da kwamishinoni da shugabannin addinai.

Sanarwar ta ƙara da cewa ƙona ƙwayoyin ya biyo bayan umarnin da wata Babbar Kotun Tarayya ta bayar.

A jawabinsa, Gwamna Umara Zulum ya ce ya kaɗu da yawan ƙwayoyin da hukumar NDLEA ta ƙwace sannan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da taimaka wa hukumar wurin yaƙi da miyagun ƙwayoyi.

Najeriya na fama da matasa maza da mata da ke ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a lungu da saƙo na ƙasar, inda hakan kan jawo rasa rayukansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.