Sojin Najeriya sun kama wasu yan Nijar dake safarar makamai a Sokoto

Sojin Najeriya sun kama wasu yan Nijar dake safarar makamai a Sokoto

Sojin Najeriya sun kame wasu ‘yan Nijar 3 a karamar hukumar Sabon Birni dake jihar Sokoto, dauke da makamai da suke kokarin safararsu ga ‘yan bindiga.


Yayin ganawa da manema labarai ranar Juma’a a birnin Abuja, babban jami’in hulda da jama’a na rundunar sojin Najeriya Manjo Janar John Enenche, yace mutanen da suka damke ‘ya’yan wata kungiyar masu fasa kaurin makamai ne ga ‘yan bindigar da suka addabi yankin arewa maso yammacin kasar.

Enenche yace an kama mutanen dauke da makaman da suka hada da bindigogi kirar AK-47 guda 8, da alburusai akalla dubu 2 da 415, boye cikin motar da suke a yankin Dantudu dake karamar hukumar sabon birni.

Rundunar sojin Najeriyar tace bincikenta na sharar fage ya nuna cewar masu safarar makaman na kan hanyar su ta zuwa kamar hukumar Isa domin mika muggan makaman ga ‘yan bindiga.

Sokoto dai na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da suka hada da Kaduna, Zamfara da Katsina, dake fama da hare-haren ‘yan bindiga a baya bayan nan inda lamarin yayi kamari a karamar hukumar Sabon Birni

Leave a Reply

Your email address will not be published.