APC ta lashe kujerun kananan hukumomi 18 a jihar Ondo

APC ta lashe kujerun kananan hukumomi 18 a jihar Ondo 

 Jam’iyyar APC ta lashe kujerun kananan hukumomi 18 a fadin jihar Ondo – Daga cikin 18 da aka saki sakamakonsu.

 kananan hukumi biyar babu abokan hamayya a zabensu, APC ce kawai tayi zabe.

 INEC ta ce an sanar da nasarar ‘yan takarar ne akan tsarin dokokin hukumar zaben jihar.

 Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe kujerun kananan hukumomi 18 a fadin jihar Ondo, a babban zaben jihar da aka gudanar ranar Asabar. 

Shugaban hukumar INEC reshen jihar, Farfesa Yomi Dinakin, ya sanar da sakamakon zaben bayan da jami’an tattara kuri’u suka karanto adadin kuri’un kowacce karamar hukuma.

 Kananan hukumomin da sakamakon zabensu yazo a sahun karshe sune Akoko ta Arewa maso Yamma, Akoko ta Kudu maso Yamma, Idanre da kuma Ondo ta Gabas. 

  Shugaban hukumar zaben ya ce ‘yan takarar jam’iyyar APC sun lashe zaben ba tare da hamayya ba, saboda APC ce kawai tayi zaben kananan hukumomin. 

Dinakin ya ce an sanar da nasarar ‘yan takarar ne akan tsarin dokokin hukumar zaben jihar ODIEC. 

Kananan hukumomin da abun ya shafa sun hada da Akoko ta Arewa maso Gabas, Ose, Ifedore, Odigbo da kuma Irele.

 Zaben kananan hukumomin an gudanar da shi ne a ranar Asabar ba tare da hamayyar sauran jam’iyyun adawa ba, kamar jam’iyyar PDP. 

Leave a Reply

Your email address will not be published.