Kananan ’Yan Kasuwa Miliyan 2.3 Ke Sha’awar Amsar Bashi – Gwamnatin Tarayya

Kananan ’Yan Kasuwa Miliyan 2.3 Ke Sha’awar Amsar Bashi – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, yawan kananan yan kasuwan da suka nuna sha’awanr amsar bashi a karkashin shiri nan na bankasa kasuwanci, sun kai miliyan 2.3

Shirin wanda gwamnatin tarayya ta bullo da shi domin a samu damar zuba jari a cikin kasar nan da kuma bunkasa kananan kasuwanci a cikin kasar nan.

 Gwamnatin tarayya dai ta bullo shirye-shirye da dama a cikin kasar nan wadanda suka hada da shirin N-power wanda ake horar da matasa ayyukan yi da ciyar da daliban makaranta da shirin bayar da basussuka.

Ministar jinkai Sadiya Umar-Farouk, ta bayyana cewa, an samar da  shirin tallafa wa kananan kasuwanci ne domin magance matsalolin kudade ga ‘yan Nijeriya sama da miliyan 37, domin bunkasa tattalin arziki a cikin kasar nan.

 Ministar ta bayyana hakan ne wajen bikin cika shekara daya a ofis a Abuja, ta kara da cewa, a cikin wadanda za su amfana da wannan shirin dai sun hada da mutanen da ke gudanar da harkokin kasuwancinsu amma ba su samu damar amsar bashi ba.

 Ta ce, a karkashin wannan shirin za a bayar da shi tsakanin naira 10,000 zuwa naira 300,000 ga kananan ‘yan kasuwa kamar masu tireda da masu sana’o’in hannu da matasa masu kere-kere da manoma da sauran ‘yan kasuwa masu sayar da mabambamtan kayayyaki.

“Tun farkon shekarar 2016 har zuwa yau, sama da kananan Yan kasuwa miliyan 2.3 ke nuna sha’awar amsar bashin domin su bunkasa harkokin kasuwancinsu,” in ji Sa’adiya Umar-Farouk.

Ministar ta kara da cew, a cikin wadanda suka amfana da shirin N-power guda 109,823 a zango na daya da na biyu, a yanzu haka sun samu nasarar bunkasa sana’o’i a cikin unguwanninsu.

“Muna samun sakamakon da muke bukata a cikin shirin N-power, a yanzu haka muna samun nasarar rage ayyukan yi duk da mutane suna kara yawa a cikin kasar nan,” in ji ta.

A bangaren ciyar da daliban makaranta kuwa, Sadiya ta bayayyana cewa, sakamakon hadakan da aka gudanar a tsakanin gwamnatin tarayya da kuma jihoji, an samu nasarar aiwatar da wannan shirin a jihohi guda 34 ciki har da Babban Birnin Tarayya.

 Ta ka da cewa, a yanzu haka yawan daliban da ake ciyarwa a karkashin wannan shirin sun kai guda 9,196,823, kamar yadda Hukumar Kididdiga ta Kasa ta bayyana, yayin da yawan wadanda suke dafa abincin suka kai guda 103,028.

 Haka kuma, ministar ta bayyana cewa, shirin  CCT ana bai wa talakawa da magidanta naira 5,000 a duk wata.

Ta ce, “tun farko ana bawa mutane wannan tallafi ba wai domin zuwan Korona bane, a cikin kididdigar da aka yi wa talakawa da magidanta mara su karfi rijista sama da miliyan 2.6 a fadin jihohi 34 da kuma Babban Birnin Tarayya.

“An dai yiwa talakawa da magidanta marasa karfi rijista sama da miliyan 3.7 a ranar 30 ga watan Yunin wannan shekarar a jihohi 36 cikin har da Babban Birnin Tarayya.”

Ministar ta kara da cewa, a yanzu haka ma’aikatarta tana shirin bayar da tallafin cutar Korona ga wadanda ta yi wa rijista da matalautan da ke burane da masu tsaka-takin talauci a yankuna daban-daban da ke cikin kasar nan. 

A cewarta, Bankin Duniya ya taimaka wajen yi wa talakawan da magidanta marasa karfi rigista wanda aka samu cikakken bayanai.

 Sadiya ta ce, gwamnatin tarayya tana kokarin tabbatar da samar da cibiyar na hukumar kula da marasa galihu.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published.