Gwamnatin kano za ta biya Naira Milyan 489.258 ga Dalibai 29,126 da zasu rubuta jarabawar NECO da NBAIS

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe Naira Miliyon 489.258 domin biya wa daliban Jihar Kano 29,126 kudin jarrabawar NECO da jarrabawar NBAIS 

 Sanarwar da jami’in yada labaran Ma’aikatar ilimi ta jIhar Kano Aliyu Yusuf ya fitar, ta ci gaba da cewa, Gwamnati zata biyawa dalibai ‘yan asalin Jihar Kano ne kadai wadanda su ka samu darajar credit biyar zuwa sama kuma ya kasance akwai lissafi da turanci a jarrabawar share fagen da ta gabata.

Haka zalika sanarwa da ta kuma sanar da cewa Gwamnatin Jihar Kano ta amince da sakin sakamakon jarrabawar share fagen da aka gudanar.

Wannan amincewa ta biyo bayan kudurin da aka gabatarwa majalisar zartarwar Jihar Kano, wanda Kwamishinan ma’aikatar limi Malam Muhammad Sunusi Sa’id Kiru ya gabatar a lokacin zaman majalisar zartarwar ta Jihar Kano da aka gudanar.

A cewar sanarwar, Gwamnati ta kuma taya daliaban murna bisa kyakkyawan sakamako da suka samu, daganan sai kwamishinan ya hori daliban da su cigaba da yabawa kokarin Gwamnatin Jihar Kano wajen ganin sun lashe jarrabawar NECO da NBAIS da kyakkyawan sakamako

Leave a Reply

Your email address will not be published.