Femi fani kayode ya ɗirkawa dan jarida zagi

Femi Fani Kayode ya tuba bayan ya sha suka daga kungiyoyin da ‘yan Najeriya

Ce-ce-kuce ya kaure bayan tsohon ministan al’adu kana tsohon
 Ministan zirga-zirgar jiragen saman Najeriya Femi Fani Kayode ya ci mutuncin wani ɗan jaridar Daily Trust, har ta tilasta masa bayar da hakuri.

Ranar Talata ne wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna tsohon ministan yana zagin ɗan jaridar, Eyo Charles, bayan ya yi masa wata tambaya yayin wata hira da ‘yan jarida.

Hasalima Mista Fani Kayode ya yi wa ɗan jaridar barazanar daukar mataki a kansa.

Eyo Charles ya tambayi Mista Kayode cewa “wane ne yake ɗaukar nauyin rangadin da kake yi a jihohin Najeriya inda kake duba ayyukan da gwamnoni ke yi?”

Tambayar ta ɓata ran tsohon minstan, inda ya rika zagin dan jaridar.

Hakan ya janyo masa suka daga bangarori da dama, ciki har da jaridar Daily Trust da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya da kuma ƙungiyar kare hakkin ɗan Adam ta Amnesty International.

Sai dai a wani saƙo da Mista Kayode ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba, ya ce ya janye kalaman da ya furta kan ɗan jaridar.


A cewarsa: “Ina da abokai da yawa ‘yan jarida waɗanda na ɓata wa rai bayan na harzuƙa da nayi amfani da zafafan kalamai. Na janye waɗannan kalaman da nayi amfani da su.”

Ya kuma bayyana cewa bai taɓa lafiyar jikin ɗan jaridar ba kuma bai tura kowa ya yi masa barazana ba. “Duk wanda yace na yi wani abu na daban ya kawo shaida.”

“Fiye da shekaru 30 da suka wuce, na yi aiki tare da kare ‘yan jarida da kuma gwagwarmayar tabbatar da ‘yanci tare da su. Ina da abokai saosai ‘yan jarida,” in ji shi.

A ranar Talata dai Mista Kayode ya fito fili ya bayyana cewa ba zai bayar da haƙuri kan irin cin mutuncin da ya yi wa ɗan jaridar ba, sai dai fitowar da yayi yanzu ya bayar da hakuri, ba ya rasa nasaba da irin wutar da ƙungiyoyi da wasu fitattun mutane suka hura wa Mista Kayode musamman a shafukan sada zumunta.

Me ya jawo ce-ce-ku-ce kan Kayode?

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ‘yan jarida da na ɗan Adam har ma da dubban ‘yan Najeriya suka yi wa Fani Kayode ca bayan ɓullar wani bidiyo da ya nuna shi yana faɗa wa ɗan jarida Eyo Charles kalaman wulaƙanci.

Lamarin ya faru a birnin Calabar na Jihar Cross River da ke Kudu maso Kudancin Najeriya.

Ɗan jaridar ya tambayi tsohon ministan cewa: “Wane ne yake ɗaukar nauyin tafiye-tafiyenka [zuwa jihohin Najeriya],” tambayar da ba tayi masa daɗi ba kuma yace “idan ka sake yi mani haka zan bige ka”.

Wane martani ake mayar wa Kayode?

Daidaikun mutane da ke amfani da shafukan sada zumunta da kungiyoyi kare hakkin dan adam sun yi matukar fusata kan batun.

Amnesty International ma ta mayar da martani kan abin da Kayode yayi inda ta nuna rashin jin dadinta.

Ta bayyana cewa Mista Eyo aikinsa yake yi kuma ‘yan jarida na nemo gaskiya ne domin mutane su sani, a cewar ƙungiyar, bai kamata a rinƙa yi musu barazana ba idan sun yi tambaya.

Ita ma ƙungiyar da ke fafutuka wajen yaƙi da cin hanci da rashawa wato SERAP ta mayar da martani inda ta ce kada wanda ya sake kiran wani ɗan jarida da irin sunan da Mista Kayode ya kira Mista Eyo.

Kuma ƙungiyar ta yi kira ga Mista Kayode da ya fito ya bayar da haƙuri inda tuni yayi hakan.

A kwanakin baya ne dai aka ba Mista Kayode sarauta a jihar Zamfara, wanda hakan ya janwo ce-ce-ku-ce har wasu masu sarautar gargajiya suka yi barazanar ajiye muƙamansu.

Mista Kayode, wanda lauya ne a Najeriya, ya taɓa riƙe muƙamin ministan al’adu sa’annan daga baya kuma ya koma ministan sufurin jiragen sama a zamanin mulkin jam’iyyar PDP a Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published.