Zulum ya fayyace dalilin da yasa yake caccakar sojojin Nijeriya

Zulum ya fayyace dalilin da yasa yake caccakar sojojin Nijeriya

Gwamnan jihar Borno,Baba gana Umara Zulum, ya ce yana sukan rundunar sojin Najeriya ne saboda su inganta yaki da suke da ta’addanci.

Zulum ya bayyana hakan a ranar Alhamis lokacin da ya kaddamar da cibiyar Tukur Buratai na yaki da zaman lafiya, wanda ke karamar hukumar Biu na jihar.

An sanya wa cibiyar sunan Tukur Buratai, shugaban hafsan sojin Najeriya.

Cibiyar wani sashi ne na jami’ar rundunar sojin Najeriya wacce ke a garin Biu.

Da farko shine wajen ajiyen kayan tarihi na rundunar sojin kasa, an samar da shi a 2016.

Gwamnan ya caccaki rundunar soji a kwanakin baya.

A watan Janairu, ya zargi dakarun soji da tatsar masu amfani da hanyoyi.

Ya kuma yi barazanar maye gurbin sojojin da maharba idan suka gaza tsare Baga biyo bayan harin da aka kai masa a watan Yuni.

Yayinda aka yarda cewa yan ta’addan Boko Haram ne suka kai harin, Zulum ya zargi jami’an sojiji da zagon kasa, inda yayi zargin cewa sune suka kai masa hari.

Sai dai, rundunar sojin ta bukaci Zulum da ya dakatar da batawa rundunar suna a furucinsa.

Da yake magana a taron kaddamarwar, Zulum ya ce ba wai baya godema kokarin sojojin bane.

Ya yi bayanin cewa, maimakon haka, zafafan zantuntuka da yake lokaci-lokaci domin karfafa masu gwiwar kara kaimi ne.

“Ba wai bana sane da inda muke bane kafin kafuwar shugabancin Buratai bane da kuma nasarorin rundunar soji wajen yaki da ta’addanci. Muna godiya da sadaukarwar rayuka da dakarun soji ke yi. 
Za mu ci gaba da marawa sojojinmu baya,” in ji Zulum.

“Idan muka sokesu lokaci zuwa lokaci, muna hakan ne domin inganta nasarorinmu ba wai rashin godiya bane.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.