SERAP ta maka Buhari da Malami da Ministar kuɗi a gaban kotu

SERAP ta maka Buhari da Malami da Ministar kuɗi a gaban kotu


Kungiyar kwatowa talakawa hakkokinsu da tabbatar da adalci (SERAP) ta maka Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari a babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja.

SERAP ta shigar da karar ne saboda gazawar Buhari na bayyana sunayen mutanen da gwamnati ta ce ta kwato N800bn daga wajensu 

 Haka zalika, kungiyar ta bukaci kotun ta tilasta wa Buhari ya fadi dalilin rabawa wasu tsiraru N51bn daga asusun gwamnati.

 A ranar 12 ga watan Yuni, 2020 Shugaba Buhari yayi jawabi mai tsayi. sakin layi 78, inda ya bayyana cewa gwamnatin sa ta kwato N800bn daga barayin kasa. 

Ya sanar da cewa an yi amfani da kudaden da aka kwato wajen gudanar da ayyukan raya kasa a sassa daban daban na Najeriya. 

A takardar karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1064/2020 da aka shigar a ranar Juma’a a kotun, SERAP ta bukaci kotun ta umurci Shugaba Buhari ya wallafa sunayen mutane da aka kwato kudaden daga wajensu. 

Haka zalika ya wallafa ranaku, da wuraren da aka yi ayyukan da har aka batar da kudaden.

 Haka zalika SERAP na son hukumomin yaki da rashawa su shigo cikin lamarin.

A cikin takardar, SERAP ta bukaci kotun ta umurci Buhari ya tilasta hukomin yaki da rashawarar su binciki yadda aka rabawa wasu tsiraru N51bn daga asusun gwamnati a shekarar 2019.

 Daga cikin wadanda ake karar akwai Abubakar Malami, Antoni Janar na kasa kuma Ministan shari’a, da Zainab Ahmed, Ministar kudi, kasafi da tsare tsaren kasa. 

Karar da SERAP ta shigar ya biyo bayan ‘yancin bayanai (FoI) da ta bukata a ranar 13 ga watan Yuni, 2020 ga Shugaba Buhari, tana mai cewa: “Al’umma na da ‘yancin sanin bayanan.

 “Yan Nigeria na da hakkin sanin yadda aka kashe N800bn da aka kwato daga mahandama da kuma dalilin rabawa wasu tsiraru N51bn daga asusun gwamnati.

 “Yin bayani dalla dalla kan kudaden da ake kashewa na da matukar muhimmanci ma damar ana son a samu fahimta da kara yarda tsakanin gwamnati da al’umar da take mulka.” 

Lauyoyi Kolawole Oluwadare da Opeyemi Owolabi, sune suka shigar da wannan kara a madadin SERAP. 

Leave a Reply

Your email address will not be published.