Sojojin Najeriya sun tarwatsa sansanin mayakan Darussalam a jihar Nassarawa

Sojojin Najeriya sun tarwatsa sansanin mayakan Darussalam a jihar Nassarawa

A makon da ya gabata ne rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun tarwatsa wani sansanin masu tayar da ƙayar baya da aka fi sani da Darussalam a yankin Uttu da kewaye da ke ƙaramar hukumar Toto a jihar Nasarawa.

Rundunar ta ce dakarunta sun farwa sansanine `yan kungiyar ne tare da haɗin gwiwar sauran jami`an tsaro, bayan sun tattara muhimman bayanai a kan maɓoyarsu.

Yayin harin, rundunar ta ce jami’anta sun yi arangama da mayaƙan kungiyar waɗanda daga bisani suka tsere, suka bar matansu, waɗanda suka miƙa wuya ga sojojin.

Kakakin cibiyar samar da bayanai a kan arangamar da sojojin Najeriya ke yi a sassan kasar Kwamanda Abdussalam Sani, ya shaida wa BBC cewa mutune fiye da dari hudu ne suka mika wuya, yawancin su mata da kananan yara.

Daga Cikin kayayyakin da sojojin suka Kama Akwai fertilizer, half a bag of gun powder, 10 locally made hand grenades, one Rocket Propelled Grenade bomb fuse, one locally made Rocket Launcher, 2 Improvised Explosive Devices,13 Improvised rocket bombs, amongst others.

Leave a Reply

Your email address will not be published.