Ana fara cike neman tallafin da Gwamnatin Nigeria zata bayar na naira bilyan 75

 Cikakken bayani game da kyautar kudi da gwamnatin shugaba Buhari zata fara bayarwa, wanda aka bude rijistan ranar Litinin da ‘karfe 10 na dare, ana so a karanta a nutse a fahimci bayanin sosai dan kada a samu matsala.

Abu na farko, wannan kudin da za’a bayar ba bashi bane, kyauta ne, Naira biliyan 75, aciki akwai Naira bilyan 15 na manyan kamfanoni da ‘yan kasuwa.


Abu na biyu, Naira bilyan 60 shine wanda ‘kananan ‘yan kasuwa da masu sana’ar hannu zasu samu.

Kashi 40 cikin 100 wadanda zasu samu wannan kyautar kudin daga shugaba Buhari mata ne.

Abu na uku:

Gwamnatin tace za a raba kuɗin ne ga masana’antu milyan daya da dubu ‘dari uku (1.3).

Sai kuma ‘yan kasuwa da masu sana’a, za’a baiwa mutane dubu 35,000 a kowace jiha daga cikin jihohi 36 na ƙasar da kuma babban birnin ƙasar Abuja.


Idan ka cire kamfanonin da suke cikin jihar ka toh banda su za’a baiwa mutane dubu talatin da biyar tallafin kudin.

Wasu zasu samu kyautar dubu 50,000 wasu 30,000


Sannan gwamnatin tace za’a bai wa mutune 250,000 damar yin rijistar kasuwancin su kyauta, zangon farko na wannan tallafi, wanda zai ɗauki wata uku, wato rijista da hukumar CAC a kyauta.

Acikin watanni uku ake fatan raba fiye da rabin kudin wato Naira biliyan 75 din.

Ga yadda tsarin zai kasance:

Ranar Litinin 21 ga watan September 2020, ranar masu kamfanoni ce, duk wanda yake so ya samu wannan tallafin idan yana da kamfani ko masana’anta toh dole sai ya cika sharudda guda hudu:

1. Na ‘daya: Dole ya zamo masana’antar ko kamfanin yana da rijista da hukumar C.A.C (Cooperate Affairs Commission).

2. Na biyu dole: Ya zamo kamfanin yana da ma’aikatan da aqalla sun kai uku (3).

.

3. Dole kamfanin ya zamo mallakar ‘dan Nigeria ne.

Dan gwamnatin tace wannan tallafin banda kamfanonin kasashen waje.

4. Dole manajan kamfanin ya mallaki lambar sirri ta banki wato BVN.

Sai ‘bangare na biyu, masu aiyuka….

Kamar Teloli, Masu aikin Ruwan famfo, masu Jan mota direbobi da masu kafinta da makamantan su.

Su Kuma za’a bude musu rijistar su ranar 25 ga wannan watan na September, idan Allah ya kaimu.

Su ba lallai sai sun yi rijista da hukumar CAC ba.

Amma dole masu sana’ar su mallaki lambar BVN da Account a bankin dake cikin Nigeria.

Sai ‘bangare na uku:

Masu kananan Sana’o’i, kamar suyan kosai, masu shagon provision, masu Noma da kiwo, masu saye da sayarwa kanana, da sauran su.

Su kuma za’a bude nasu rijistan ranar 28 ga wannan wata na September.

Su ma ba lallai sai suna da rijista da hukumar CAC ha.

Amma dole su mallaki lambar BVN da account a wani bankin dake cikin Nigeria.


Taba link ka Nemi tallafin

Https://survivalfund.ng

Ko Kuma 

Www.survivalfundapplication.com

DOMIN TAMBAYA KO NEMAN KARIN BAYANI ZAKU IYA KIRA,TURO SAKON KARTA KWANA TA 08130075757 KO TA WHATSAPP

https://wa.me/message/ZBA37PUSO35VM1

Leave a Reply

Your email address will not be published.