Za a buɗe makarantu ranar 11 ga watan Oktoba a Bauchi


 Za a buɗe makarantu ranar 11 ga watan Oktoba a Bauchi


Gwamnatin jihar Bauchi ta ce makarantun firamare da sakandare za su bude daga ranar 12 ga watan Oktoba mai kamawa.


Dole ne malamai da Dalibai su saka takumkumin Baki da hanci domin dakile yaduwar cutar korona.


An rufe makarantun ne a cikin matakan dakile cutar korona kimanin watanni shidda da suka wuce.


Cikin wata hira da kwamishinan ilmi na jihar Bauchi Dr Aliyu Tilde, ya shaida wa BBC cewa Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir ne ya ba da izinin bude makarantun bayan da suka tattauna kan batun.

Leave a Reply

Your email address will not be published.