El Rufa’i ya soke zaɓen farko na masu zaɓen sabon sarkin Zazzau

 


El Rufa’i ya soke zaɓen farko na masu zaɓen sabon sarkin Zazzau


Yunƙurin farko na naɗa sabon Sarkin Zazzau ya ci tura, inda a yanzu haka masu zaɓe na Masarautar Zazzau suke sake nazari kan sabon matakin zaɓen Sarki.


A ranar Laraba da yamma ne gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufa’i ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa, ”A yanzu haka masu zaɓen sarki na sake sabon nazari don zaɓo waɗanda za a zaɓa cikinsu da zai zama Sarkin Masarautar Fulani ta Zazzau na 19.


”Gwamnatin jihar Kaduna ce ta bayar da umarnin yin sabon zagaye na zaɓen bayan da ta soke na farko da aka fara, inda aka cire ƴan takara biyu.


A sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar, ta bayyana cewa soke zaɓen farkon na da alaƙa da cire sunayen wasu ‘yan takara biyu waɗanda suka nuna sha’awar sarautar amma daga baya aka ce musu an rufe karbar sunayen masu son zama sarki.


Cikar Najeriya shekaru 60 Buhari ya yi amai ya lashe

https://www.arewagist.com.ng/2020/09/cikar-najeriya-shekaru-buhari-ya-yi.html?m=1

Gwamnatin jihar ta kuma nuna ɓacin ranta dangane da yadda aka tsegunta batun zaɓen da masu zaben sarki suka yi a ranar 24 ga watan Satumba tun kafi gwamnan jihar ya samu rahoto a hukumance kan zaɓen.


A ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba ne Sarkin Zazzau Dakta Shehu Idris ya rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.


Tun bayan rasuwar sarkin, gwamnan jihar ya tsiri karatun litattafai daban-daban inda a halin yanzu ya karanta aƙalla litattafai uku kamar yadda ya bayyana.


Ya ce littafan za su taimaka masa wurin yanke hukunci a zaɓen sarkin ganin cewa shi ne mai wuƙa da nama a ƙarshen zaɓen.

An fara cike neman tallafin da Gwamnatin Nigeria zata bayar na naira bilyan 75

https://www.arewagist.com.ng/2020/09/yadda-zaka-sami-tallafin-da-za-bayar-na.html?m=1

Leave a Reply

Your email address will not be published.