Trump da matar sa sun kamu da cutar korona

 


Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shi da matar sa Melania sun kamu da cutar korona.


Trump ya sanar da haka ne a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis da tsakar dare a agogon Amurka.

Likitan Mr Trump, Sean Conley, ya fitar a sanarwa yana mai cewa shugaban kasa da mai dakinsa “suna cikin koshin lafiya a wannan lokaci, kuma sun ce za su ci gaba da zama a gidansu na White House domin yin jinya”.


“Ina mai tabbatar muku cewa shugaban zai ci gaba da gudanar da ayyukansa ba tare da wata matsala ba a yayin da yake murmurewa, kuma zan rika sanar da ku halin da suke ciki nan gaba,” in ji sanarwar.

Tun da farko a ranar Alhamis, Mr Trump ya ce shi da mai dakinsa, wacce ke da shekara 50, za su killace kansu bayan hadimarsu Ms Hicks ta kamu da cutar korona.


Hicks, mai shekara 31 da haihuwa, ita ce mai yi wa shugaba Trump hidima mafi kusanci da shi da ta kamu da cutar kawo yanzu.


Ta bi shugaban zuwa jihar Ohio a makon jiya cikin jirginsa na Air Force one lokacin da aka yi wata muhawara tsakaninsa da Joe biden a farkon makon nan.


An nuna hotunanta tana shiga jirgin saman shugaban kasar ranar Talata a Cleveland kuma ba ta sanye da takunkumi.


Daga baya kuma ta bi shugaban cikin jirginsa mai saukar ungulu mai suna Marine One ranar Laraba lokacin da ya tafi wani gangamin siyasa a Minnesota.


Hope Hicks ta rike mukamin shugabar ofishin sadarwa a Fadar White House a 2017 – 2018


Me Shugaba Trump yace?

Mr Trump ya wallafa sakon Twitter ranar Alhamis yana cewa: “Hope Hicks, wacce take aiki tukuru ba tare da daukar hutu ko kankane ba, ta kamu da Covid 19. Abin bakin ciki!


“Mai dakina da ni muna jiran sakamakon gwajin da aka yi mana. Amma kafin nan, za mu killace kanmu!”


Babu tabbaci kan yadda killacewar za ta shafi muhawarar shugaban kasa ta biyu za ta kasance, wacce za a gudanar ranar 15 ga watan Oktoba a Miami, jihar Florida.


A yayin da yake waya da dan jaridar Fox News Sean Hannity ranar Alhamis da daddare, Mr Trump ya ce shi da mai dakinsa “sun kwashe tsawon lokaci tare da Hope”.


“Don haka za mu ga abin da zai faru,” a cewar shugaban, yana mai karawa da cewa Ms Hicks tana yawaita sanya takunkumi amma ga shi ta kamu da cutar korona.


Jaridar The Hill da ke bayar da labaran siyasa ta ambato wata majiya a Fadar White House tana cewa an soma bibiyar mutanen da suka yi mu’amala da ita kuma an sanar da kowa abin da suke kamata suyi”.


Shin akwai karin wadanda suka kamu da cutar a White House?


Ms Hicks ita ce babbar makusanciya a White House ta baya bayan na da ta kamu da Covid-19. 


Sakatariyar watsa labaran mataimakin shugaban kasa Mike Pence Katie Miller ta harbu da cutar a watan Mayu amma ta warke.


Kazalika a watan na Mayu, wani mamba na Rundunar Sojin Ruwan Amurka da ke aiki a tawagar Mr Trump ya kamu da cutar.


Amma fadar White House ta shugaban kasar da mataimakin sa Basu kamu da cutar ba.

1 thought on “Trump da matar sa sun kamu da cutar korona

Leave a Reply

Your email address will not be published.