Naira Milyan 9,300,000 Muke karba Duk wata – Dan Majalisa ya fasa kwai

 


Ɗan Majalisar Tarayya Simon Karu, ya fallasa cewa naira milyan 9 da naira 300,000 kowane Ɗan Majalisar Tarayya ke karɓa kowane wata, sanatoci Kuma Milyan 13 da 500,000.

Karu, wanda ke wakiltar Kananan Hukumomin Kaltungo da Shongom a Jihar Gombe, ya yi wannan jawabi a taron murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun ƴancin kai.


Sai dai kuma ya ce amma wadannan kudade da ake ba su, duk suna tafiya ne wajen biyan bukatun ‘yan mazabar su masu damun su da roko, bukatun dole, na yau da kullum, agaji, tallafi da maula.


Karu wanda ke daya daga cikin manyan baki masu jawabi a wurin taron, ya ce kudaden su na albashi da na tafiyar da ayyukan office duk suna cikin wadannan milyan 9.3 din da ake bai wa kowanen su a duk karshen wata.


Du dudu albashin Dan Majalisar Tarayya a duk wata bai wuce naira 800,000 ba. Na fada muku zan fadi wanan batu. Me yasa baza ku jira na fada ba?


Sauran naira milyan 8.5 kuma Kuɗaɗen tafiyar da ayyukan ofis ne.


“Waɗan sun ku da suke da masaniyar yadda abin ya ke, sun sani cewa yadda na fada haka adadin yake.


“Inda matsalar take, shi ne ‘yan ba ni, ba ni da ‘yan maula sun yi yawa a mazabun da mu ke wakilta. To da zaran an nema a wurin ka, ba a samu ba, sai a fara bata ka, ana yi maka yarfe da sunayen banza daban-daban


Kafin na hau kan mimbarin jawabin nan, an turo min e-mel uku daga mazaba ta. Wasu neman kudi wani kuma neman aiki. To da na ce ba za a samu ba, to shikenan abin ya zame min matsala.”


Karu ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa ya furta kalamin a wurin taron.


Sai dai kuma wani Dan Majalisar Tarayya Nicolas Osai, ya karyata Hon. Karu.


“Ni dai ba a taba ba ni wannan adadin kudin a matsayin albashi ba. Kuma na riga shi zuwa Majalisa.” Inji shi.


Domin siyan DATA Ta MTN da take yin wata daya 1GIG akan 360 Yi magana ta WhatsApp 08122225296

Leave a Reply

Your email address will not be published.