Atiku ya buƙaci a dauki mataki kan rundunar tsaro ta SARS


 Atiku ya buƙaci a dauki mataki kan rundunar tsaro ta SARS


Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya bi sahun wadanda suke kira ga gwamnati ta dauki matakin da ya dace kan wannan runduna, “inda yace an kafa tane domin yaƙi da manyan laifuka irinsu fashi da makami da satar mutane.


Amma a yanzu sun koma farwa mutane masu neman na kansu.”


Wannan ya biyo bayan rahotannin da wasu daga cikin jaridun Najeriya suka wallafa, da kuma wani hoton bidiyo da ya nuna wasu da ake zargin jami’an rundunar SARS ne sun kashe wani mutum tare da guduwa da motarsa.


Lamarin ya faru ne a ranar Asabar 3 ga watan Oktoba a kofar wani Otel da ke kira Wetland, a garin Ughelli da ke Jihar Delta.


Cikin bidiyon an nuna jami’an da ake zargi sun dauki motar mutumin da suka kashe kirar Lexus SUV.


Taba link kakalli yadda ƴan Sandan Suka kashe mutumin

https://youtu.be/gnSfWeQJGDQ

Ba wannan ne karo na farko da ake samun takun saƙa tsakanin ƴan Najeriya da rundunar SARS ba, kan irin ayyukan da rundunar ke yi, waɗanda mutane ke zargin cewa zalunci ne zalla.


A shekarar 2017 an yi ta kiraye-kirayen a soke rundunar inda har akayi ta zanga-zangar a wasu biranen Najeriya, bayan gangamin da aka rika yi a shafukan zumunta na neman a rushe ta bisa zargin taka hakkin bil’adama.


Ammam a martanin da ta mayar a watan Disamban 2017 rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce babu wani abu da zai sa ta rusa rundunar ta ta musamman mai yaki da fashi da makami da ake kira SARS duk da kiraye-kirayen da wasu a kasar ke yi na soke ta


Domin siyan DATA Ta MTN da take yin wata guda 1GIG akan 3550 Yi magana ta WhatsApp a 08122225296

Leave a Reply

Your email address will not be published.