Kasafin kudin Najeriya na shekarar 2021 ya zarce na 2020 da naira triliyan 3


Kasafin kudin Najeriya na shekarar 2021 ya zarce na 2020 da naira triliyan 3


Shugaban Najeriya Muhammadu ya mika wa majalisar dokoki kasafin kudin shekarar 2021 wanda ya kunshi naira triliyan 13 domin gudanar da manya da kuma kananan ayyukan raya kasa.


Ministar kasafin kudi da tsare-tsare Zainab Shamsuna ta ce sunyi iya bakin kokarin su, sun fitar da abinda suke ganin zai yi wu.


Ta ce kashe Naira Tiriliyan 13 ga gwamnatin tarayya kudi yan kadan, saboda idan ka canja su zuwa Dala $35,000 kenan.


Mahukuntan Najeriya sun ce gwamnati ta ci nasarar aiwatar da akalla kashi %68 cikin 100 na kasafin kudin 2020 a watan satimba. 


Anyi kasafin kudin 2021 bisa fatan za a siyar da gangar man fetir a kan dalla 40


 Mai sharhi kan al’amuran yau da kullum yusha’u Aliyu cewa yayi dala 40 da akayi tsammanin za a siyar da gangar man fetir a kasafin zai iya yin tasiri ganin yadda Hukumar OFEC take kokarin kayyade man da ake kaiwa kasuwa.


sannan ana sa ran kamfanonin da annobar korona ta durkusar da su, za su farfado gaba daya. 


Ya ce hasa she ya nuna duk lokacin da ƙasa tayi rashin lafiyar tattalin arzikin, to yana warkewa da karfin sa.


Sanata Ahmed baba kaita da ke wakiltar Daura cewa yayi nauyi ya Koma kansu, domin suyi aiki Kan Wannan kasafin kuɗi, su kammala kafin sabuwar shekara.


Domin siyan DATA Ta MTN da take yin wata daya 1GIG akan 350 Yi magana ta WhatsApp 08122225296

Leave a Reply

Your email address will not be published.