Wata Mata ta yanka ƴaƴan ta Saboda Zafin An Mata Kishiya

 

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wasu yara biyu da ake zargin mahaifiyarsu ta yi musu yankan rago.


‘Yan sandan sun ce ana zargin cewa matar ta sami sabani da mijinta saboda ya yi mata kishiya a watanin baya.


Wannan lamari ya faru ne a unguwar Sagagi Layin ‘Yan Rariya da ke kwaryar birnin kano.


Yaran da ake zargin mahaifiyar su ta yanka su, su ne Yusuf Ibrahim mai shekaru biyar da yar uwarsa Zahra’u Ibrahim mai shekaru uku kuma sun gamu da ajalin nasu ne a jiya Asabar.


Lamarin ya daurewa mutane da dama kai a unguwar ta Sagagi da ma fadin jihar Kano, musammam ga makotan gidan da lamarin ya faru inda suke cewa a iya sanin da suka yi wa matar bata da tabɓin hankali haka kuma ba a santa da shaye-shaye ba.

Amma sai dai wasu, sun kuma alakanta abin da matar tayi da kishiyar da mjin ta yayi mata a ‘yan kwanakin baya, wanda har ta kai ga sun samu rashin jituwar da ya janyo mutuwar aure, amma daga baya aka dai-dai ta ta koma dakinta.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin mahaifin yaran da aka kashe ma’ana mijin matar da ake zargi da kashe ‘ya’yan natan, amma bai iya magana ba saboda yanayi na juyayi da alhi ni da yake ciki sakamakon abin da ya faru.


Wani lamarin da yake kara daure kai a cikin batun shi ne rashin sanin inda matar take da kuma halin da take ciki, domin a cewar kakakin rudunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Haruna Kiyawa abin da suka sa gaba yanzu shi ne neman inda matar take, domin tuni suka kaddamar da bincike.


Tuni dai aka yi wa yaran jana’iza a dai-dai lokacin da ake ci gaba da neman mahaifiyarsu da ake zargin ita ta raba su da duniya, bayan ta sha wahalar daukar cikinsu da rainonsu har suka fara zama mutane.


Lamarin dai ya dauki hankulan jama’a da dama musamman ganin irin shakuwar da ke tsakanin ɗa da mahaifi, abin da wasu ke ganin ruwa ba ya tsami banza, kuma dalilin kishi bazai sa uwa ta hallaka ‘ya’yanta ba, don haka mutane ke fatan samun takamemen amsa duk lokacin da aka samu matar da ake zargi aka kuma gudanar da bincike.

DOMIN SIYAN DATA TA MTN DA TAKE YIN WATA GUDA YI MAGATA TA WHATAPP A 0822225296

Leave a Reply

Your email address will not be published.