Matar da ake zargi ta kashe ƴaƴanta a Kano ‘tana da aljanu’

 


Matar da ake zargi ta kashe ƴaƴanta a Kano ‘tana da aljanu’


Rundunar ƴan sandan Kano ta ce tana tsare da matar


Mahaifiyar matar da ake zargi ta kashe ƴaƴanta guda biyu a jihar Kano  ta ce ƴarta ta daɗe tana rashin lafiyar da ke da nasaba da iskokai.


A ranar Asabar ne rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wasu yara biyu mace da namiji yan shekara uku da kuma shida da ake zargin mahaifiyarsu ce ta kashe su.


Lamarin wanda ya faru a Unguwar Sagagi Layin ‘Yan Rariya a birnin Kano, da farko an bayyana cewa sun sami saɓani ne da mijinta saboda ya yi mata kishiya a watannin baya yakai ga kisan ƴaƴansu.


Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce jami’anta sun kama matar yanzu haka tana hannunsu, kuma ta tabbatar da cewa ita ta kashe ƴaƴanta, kamar yadda kakakin rundunar ya shaida wa BBC.


Ya kuma ce bayan matar ta kashe yayanta biyu ta kuma raunata wata yarinya yar shekara 10.


Amma kakar yaran da aka kashe Binta Ado Nababa ta shaida wa BBC cewa ƴarta ta shafe tsawon wata uku ba ta iya bacci, “tana cewa kullum da daddare ana zuwa ana danne ta ana shake ta. Ta fi wata uku ba ta bacci, da daddare ana yi mata gurnani irin na dodanni.”


“Da farko ban ɗauki maganarta da muhimmanci ba amma na faɗa mata cewa ta dinga yin addu’a kuma ta faɗa wa mijinta,” in ji mahaifiyar matar.


Sai dai mahaifiyar ta ce tun da ta aurar da ƴarta shekara shida da suka gabata, ƴarta take tafka rikici da mijinta. “Kullum faɗa suke da mijinta,” in ji ta.


Mahaifiyar ta ce ta taɓa zuwa neman kashe auren ƴarta saboda rikicin da kullum suke yi da mijinta.


“Saboda ita ta huta da rikicinta da suke yi da mijinta. Wata ɗaya da zuwa gidansa suke tafka rigima, kuma irin rikicin da suke yi ne har dangin mijin suke tunanin akwai abin da ke damunta,” in ji ta.


Mahaifiyar ta kuma ce daga baya ƴarta ta samu rashin lafiyar, kuma ƴarta ta taɓa zuwa wurin malami har aka yi mata karatu amma rashin lafiyar ya ƙara tsanani.


Yadda Yan Sanda SARS Suka kashe Wani, Kuma Suka gudu da Motar sa

https://youtu.be/gnSfWeQJGDQ


Abin da mahaifin matar ya ce kan kisan jikokinsa

Muna zaune kwatsam mijin ya shigo jikinsa duk jini, matarsa na zaune a daki sai na leƙa naga duk jikinsa jini sai ya ce kashe ƴayanta tayi ta gudo.


Sai ta rantse tace “wallahi tallahi ba ita ta kashe suba kuma bata san wanda ya aikata kisan ba.”


Data zo nan gidan ta ce baza ta iya kwana ba kowa a gidan ba. Ta ce tsoro take ji, tana son a ba ta babba da za ta iya zama dashi.


Lokacin data shigo na tambaye ta, ko lafiya tazo, ta ce lafiya lau ba komai. Amma zazzabi take ji ba ta da lafiya.


Da mijin yazo sai ya ce matarsa ta yi masa waya cewa, yazo yaga yayanta za su kashe ta.


Uwar ta ce bata san yanzu inda ƴarta take ba, tun lokacin da mijinta ya tafi da ita.


Sufeton Ƴan Sanda Ya Haramta Wa Rundunar SARS Kafa Shingayen Bincike.

https://www.arewagist.com.ng/2020/10/sufeton-sandan-ya-haramta-wa-rundunar.html?m=1

Abin da ƴan sandan Kano suka ce

Kakakin Rundunar ƴan sandan Kano Abdullahi Haruna ya ce ba yanka ƴaƴanta tayi ba, sassara su tayi da adda da taɓarya.


Ya ce bayanan da suka samu sun taimaka har sun kama matar misalin karfe 10:30 na dare bayan ta gudu.


Ta shaida wa ƴan sanda cewa yaran ne suka ɗauki wuka suna neman halaka ta, daga nan kuma ta shiga dukansu da taɓarya da kuma sassara su da adda.


Ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar Kano ya bayar da umurni a dawo da ita babban sashen binciken kisan kai domin faɗaɗa bincike. Kuma za su cigaba da bincike kan abin da yasa ta aikata kisan.


Haka kuma ƴan sandan za suyi bincike kan mijin domin gano ko yana da hannu a aikata kisan.


Lamarin ya daure wa mutane da dama kai a unguwar ta Sagagi da ma fadin jihar Kano, musamman makwabtan gidan da lamarin ya faru, inda suke cewa a iya sanin da suka yi wa matar ba ta da taɓin hankali, haka kuma ba a san ta da shaye-shaye ba.


Kasafin kudin Najeriya na shekarar 2021 ya zarce na 2020 da naira triliyan 3

https://www.arewagist.com.ng/2020/10/kasafin-kudin-najeriya-na-shekarar-2021.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.