Gwamnatin Kaduna ta Naɗa Sabon Sarkin Masarautar Zazzau

 

Gwamnatin Kaduna ta Naɗa Sabon Sarkin Masarautar Zazzau


Gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya ta naɗa Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau.


Sakon da aka wallafa a shafin gwamnatin jihar na Twitter, ya ce “Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da nada Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19.


Ya maye gurbin Mai Martaba Alhaji (Dr.) Shehu Idris wanda ya rasu ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba 2020, bayan ya kwashe shekara 45 yana kan mulki.”

“Alhaji Bamalli shi ne sarki na farko daga gidan Mallawa cikin shekara 100 da suka gabata, bayan rasuwar kakansa Sarki Dan Sidi a shekarar 1920,” a cewar sanarwar.


Ta kara da cewa: “Malam Nasir El-Rufai ya taya Mai Martaba Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli kan nadin nasa kuma ya yi masa fatan alheri da zaman lafiya a mulkinsa”.

Miliyoyin ƴan Najeriya na cikin matsanancin talauci – Osinbajo

https://www.arewagist.com.ng/2020/10/miliyoyin-najeriya-na-cikin-matsanancin.html

Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli shi ne Magajin Garin Zazzau kuma jakadan Najeriya a kasar Thailand kafin nadinsa a matsayin sarki.


Ɗa ne ga Nuhu Bamalli, Magajin Garin Zazzau, kuma tsohon minista a Najeriya, wanda ya rasu a 2001.


A makon jiya ne gwamnatin Kaduna ta ce masu zaɓen sarki za su sake tattaunawa domin zaɓen wanda ya dace bayan an soke zaɓinsu na farko saboda “sun cire mutum biyu da ke takara”.


A ranar 24 ga watan Satumba ne Gwamna El-Rufai ya ce yayin da yake jiran sunaye daga masu zaɓen sarkin Zazzau, yana karanta wani littafi na wani Farfesa farar fata kan zaɓen sabon sarkin Zazzau.


A shafinsa na Twitter, El-Rufa’i ya wallafa hoton bangon littafin da Farfesa M G Smith ya rubuta mai taken “Gwamnati a Zazzau” wanda aka wallafa a 1960.


Gwamna El- Rufa’i ya ce littafin da ke bayani kan zaɓen sarakunan Zazzau daga 1800 zuwa 1950 zai yi masa jagora wajen yanke shawarar zaɓen sabon sarkin Zazzau.

Daga bisani ya samu ƙarin littattafai waɗanda ya karanta domin ya samu ƙarin fahimta kan yadda zai yi adalci wajen zaɓen sarkin na Zazzau.

Domin siyan DATA Ta MTN da take yin wata daya 1GIG akan 350 Yi magana ta WhatsApp a 08122225296 ko Kira a 08107747229

Leave a Reply

Your email address will not be published.