Majalisa ta shawarci Buhari ya soke wasu hukumomi Kan Zirarewar kuɗaɗe ta Ɓangarorin

 


Majalisa ta shawarci Buhari ya soke wasu hukumomi Kan Zirarewar kuɗaɗe ta Ɓangarorin


 Sanatoci sun shawarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya soke wasu hukumomi da ke zaman kawai


 Majalisar dattijai ta ce gwamnati baza ta samu wasu manyan kudade ba idan aka rage kasafinta 


Gwamnatin tarayya na yawan korafin cewa tana kashe makudan kudi wajen gudanar da ma’aikatu da hukumominta.


 A cewar majalisar, hakan zai taimakawa gwamnati wajen rage yawan adadin kudaden gudanarwa da take kashewa. 


Wannan shawara na kunshe ne a cikin rahoton tsarin dabarun tafiyar da gwamnati daga 2021-2023 da majalisar dattijai ta amince da shi. 


Gwamnatin Kaduna ta Naɗa Sabon Sarkin Masarautar Zazzau

https://www.arewagist.com.ng/2020/10/gwamnatin-kaduna-ta-naa-sabon-sarkin.html

Shugaban kwamitin harkokin kudi a majalisar dattijai, Sanata Solomon Adeola, ne ya gabatar da rahoton a gaban majalisa.


 Bayan mambobin majalisar sun amince da rahoton, shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan, ya ce irin wadannan hukumomi sun zama hanyar zirarewar kudaden gwamnati. 


 Lawan ya bayyana cewa majalisa za ta hada kai da bangaren zartarwa domin zakulo irin wadannan hukumomi. “Da yawa daga cikin wasu hukumomi an kirkiresu ne domin wata matsala ko bukata a wani lokaci. 


 “Yanzu basu da wani tasiri balle sauran katabus, sun zama hanyar zirarewar kudaden gwamnati duk shekara. 


“Za mu hada kai da bangaren zartarwa domin zakulo irin wadannan hukumomi. 


Na san hakan zai haifar da rudani da cece-kuce. “Ba aiki ne mai sauki ba, na san za a zargemu da yunkurin raba jama’a da aikinsu, amma ya zama dole mu nemi hanyar rage zurarewar kudaden gwamnati. 


“Rage kasafin kudin majalisa ba zai karawa gwamnati wasu kudi ma su yawa ba, kasafin majalisa N128bn ne daga cikin kasafin kasa N13trn,” a cewar Lawan. 


Domin siyan DATA Ta MTN da take yin wata daya 1GIG akan 350 Yi magana ta WhatsApp a 08122225296 ko Kira a 08107747229

Leave a Reply

Your email address will not be published.