Shugaba Buhari Ba Shi Da Ikon Sake Fasalin Nijeriya – Tanko Yakasai


 
Shugaba Buhari Ba Shi Da Ikon Sake Fasalin Nijeriya – Tanko Yakasai


Daya daga cikin manyan dattawan ’yan siyasa a Nijeriya, Alhaji Tanko Yakasai, ya bayyana cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba shi da ikon sake fasalin tsarin mulkin Nijeriya.


Don haka ya shawarci masu rajin ganin an sake fasalin zaman takewar kasar da su tuntuɓi wakilansu a majalisu na jihohi da na tarayya, domin cimma burin su na sake fasalin kasar nan.


Yakasai, wanda yayi magana a cikin wata tattaunawa da akayi dashi ta wayar tarho da Wakilin LEADERSHIP A YAU a Abuja, yana cewa, “Shugaban Kasa ba shi da ikon aiwatar da sake fasalin zaman takewar Nijeriya.


“Zai dai iya gabatar da doka kamar kowane dan Nijeriya ya aike da ita zuwa ga majalisun kasa domin su duba.


“Zan so na bai wa masu rajin neman a sake fasalin zaman takewar kasar nan da su aike da bukatun su zuwa ga majalisun kasa, su matsa wa wakilansu da suyi abin da ya dace.


“Akwai bukatar mubi hanyoyin da suka dace domin cimma manufa. A yanzu haka muna tafiyar da tsarin mulki ne na dimokuradiyya wanda ya bukaci tattaunawa da shawarwari a tsakanin al’umma.


Alhaji Tanko Yakasai, ya yi nu ni da cewa, zai fi wa Nijeriya kyau in har za a rika tattaunawa ana cimma yarjejeniya a tsakanin ‘ya’yanta.


In dai ba a manta ba, babban shugaban Cocin nan na Redeemed Christian Church of God, Pastor Enoch Adeboye, da wasu mutane masu yawa a ranar Asabar sun yi kira ga gwamnatin tarayya a karkashin shugaba Buhari da ta hanzarta aiwatar da sake fasalin zaman takewar kasar nan a cikin hanzari domin gujewa fashewar kasar.


Cikin amsar da fadar shugaban kasan ta bai wa masu wadannan kiraye-kirayen wanda mai Magana da yawun fadar shugaban kasan, Garba Shehu ya sanya wa hannu tana cewa, “Muna gargadi ga marasa kishin kasar nan wadanda basa yin fatan alheri a kan wannan gwamnatin, muna sanar da su cewa wannan gwamnatin baza ta taba rusunawa ga duk wata barazanar da suke yi mata a kan batun sake fasalin zamantakewar kasa ba, a daidai lokacin da wannan gwamnatin ta mayar da hankalinta wajen inganta yanayin tsaro a cikin kasar nan da kuma fuskantar matsalolin lafiya da annobar korona ta haifar mana.

Domin siyan DATA Ta MTN da take yin wata daya 1GIG akan 350 Yi magana ta WhatsApp a 08122225296 ko Kira a 08107747229

Leave a Reply

Your email address will not be published.