Gwamnatin Najeriya ta bude shafin Neman tallafin bashin biliyan 75


 A Wannan makon Buhari ya kaddamar shirin N-YIF domin matasa masu kasuwanci suyi rijista dan samun bashin. 


Babban Bankin Nijeriya ne ya dauki nauyin shirin da ma’aikatar ci gaban matasa da wasanni da nufin saka jari ga matasa masu son yin kasuwanci a kasar, domin bunkasa tattalin arziki da kuma samar musu da ayyukan yi.


Bayanan da gwamnati ta fitar ta ce sai ƴan tsakanin shekara 18 zuwa 35 da suke son yin kasuwanci kuma suke bukatar tallafin kudi.


Tallafin kudin ya shafi zuba jari ga matasan da suke da burin kasuwanci da basirar da suke da ita.


Gwamnati ta yi imanin cewa za ta sauya tunanin matasan su koma dogaro da kansu ta yadda za su taimaka wa ci gaban kasa.

Shirin na tsawon shekara uku ne.


Mai taimaka wa shugaban kasa a ɓangaren kafofin sadarwa na intanet, Lauretta Onochie, ta bayyana cewa matasan da ke son neman tallafin za su shiga wannan link din domin su nema.

https://nyif.nmfb.com.ng


Amma kafin cike fom din neman bashin dole sai mutum ya tabbata yana da lambobin banki na—-> BVN.


Gwamnati za ta saki naira biliyan 25 duk shekara har shekara uku da za a kammala shirin.


Ministan matasa da wasanni Sunday Dare, ya ce matasa 500,000 za su amfana da shirin duk shekara tsakanin 2020 zuwa 2023.


Kuma ya ce shirin na gwamnatin na da burin magance matsalar rashin ayyukan yi ga matasa.


Wanda bai yi rijistar kasuwancin ka ba zai iya samun tallafin kudin kimanin Naira dubu dari biyu da hamsin (N250,000) sai kuma wandanda suka yi rijistar kasuwancinsu da hukuma ko masu “Company Limited Liability” zasu iya samu kimanin miliyan uku (N3,000,000)


Sai dai a wannan shiri dole sai mutum ya samu Certificate na Training daga daya daga FEDERAL MINISTRY OF YOUTHS AND DEVELOPMENT ENTREPRENEUR DEVELOPMENT INSTITUTE (FMYD EDI).


Wannan Training din online ne kamar yadda suka sanar, kuma zai dauki tsawon kwana 5 kafin a kammala, idan mutum ya gama za’a turo masa Certificate na shaidar yin training din online, wanda kuma sai da shi Online certificate din zaka samu wannan tallafi.


Wannan Training din wanda za’a yi yana da sauki kwarai da gaske.


Ga yadda za kayi training din:

(1) Za kayi downloading din Application na “ZOOM” a Play store, shine application da zaka rika halartar tarurruka ta online, ko karatun littattafai.


(2) Sai kayi sign-up, wato rijista.


(3) Lokacin da za kayi Training N-YIF din zasu turo maka da Username da Password, ko kuma su turo maka link din da zaka shiga zai kaika inda ake Training online.


Zaka rika kallon videon yadda ake training ‘din, kuma zasu rika turo maka tambaya game da abunda suke tattaunawa a kai kuma kana basu amsa (Yawancin tambayoyin Objectives ne) wato chanki-chanki na A, B, C ko D a matsayin amsa.


Idan kuma mutum ya wuce shekaru 35 ba zai samu damar shiga wannan program din ba, ko namiji ko mace, haka kuma idan mutum bai kai shekaru 18 ba shima ba zai samu damar shiga Shirin ba.


An tabbatar da cewa duk wanda yayi wannan training din na Kwana 5 zai sami wannan tallafin.

Idan ba kayi Register taɓa kayi Rijista

https://nyif.nmfb.com.ng

1 thought on “Gwamnatin Najeriya ta bude shafin Neman tallafin bashin biliyan 75

  1. Wlh ni nayo download din application din na ZOOM amma wajan create din password na karshe yayi man wahala na rasa yanda akeso ya kasan ce ko za a taimaka man ayiman baya ni yanda zanyi sa

Leave a Reply

Your email address will not be published.