Zanga-Zanga ta ɓarke a kano baƴan Sanda sun kashe wani Matashi

 


Ana zargin ‘yan sandan Anty daba da kashe matashi a Kano ranar Lahadi


Cincirundon matasa sun hau titi a Kano domin nuna ɓacin ransu sakamakon kisan wani matashi da ake zargin ‘yan sanda da yi.


Matasan sun yi zargin cewa ‘yan sanda sun je kama mutum biyu a Unguwar Ƙofar Mata, inda suka kashe ɗaya daga cikinsu sannan ɗayan ya tsere.


BBC ta tuntunɓi kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, sai dai ya ce bazai iya yin magana ba ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.


Masu zanga-zangar sun ƙona tayoyi a kan titin Ƙofar Mata da ke ƙwaryar birnin Kano. A yanzu haka an rufe hanyar zuwa Kasuwar Kantin Kwari.


Lamarin na zuwa ne yayin da aka shafe mako biyu a jere ana zanga-zangar Allah-wadai da cin zarafin da ‘yan sanda ke aikatawa a kusan dukkanin jihohin Najeriya, abin da ya haddasa rushe rundunar SARS mai yaƙi da fashi da makami.


Gwamnatin Najeriya ta bude shafin Neman tallafin Bashin Naira Bilyan 75

https://www.arewagist.com.ng/2020/10/wannan-makon-buhari-ya-kaddamar-shirin.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.