Yadda Zanga-zanga ta haifar da tashin hankali a Jos

 


Yadda Zanga-zanga ta haifar da tashin hankali a Jos


An ƙone motocin mutane a rikicin na Zanga-zanga a Jos


Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Filato na cewa an samu hatsaniya yayin zanga-zangar EndSARS a sassan birnin.

Bayanai na cewa masu zanga-zangar ba su samu damar shiga cikin birnin Jos ba tun lokacin da suka fara zanga-zangar, sai a yau Talata ne suka kutsa kai cikin birnin da nufin tsayar da al’amura inda suka tare babbar hanyar Ahmadu Bello, lamarin da ya haifar da arangama tsakaninsu da wasu matasa.

Rahotanni sun ce an ji karar harbe-harbe a yankin, lamarin da ya tilasta wa mazauna unguwar rufe shagunansu da kuma ƙauracewa tashin hankalin.


Leave a Reply

Your email address will not be published.