An Bankawa hedikwatar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa Wuta a Legas


 An Bankawa hedikwatar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa Wuta a Legas


An cinna wuta aa hedikwatar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa da ke Marina a Legas inda ake zargin ‘yan daba da suka fustata ne suka yi hakan.


Babu wani cikakken bayani kan yadda aka cinna wutar ga hukumar ta NPA, amma wani bidiyo da kafar talabijin ta AIT a Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter ya nuna yadda ginin ke ƙonewa.


Ko a safiyar yau sai da aka cinna wuta ga gidan talabijin na TVC da kuma tashar mota ta Oyingbo a jihar ta Legas.

Leave a Reply

Your email address will not be published.