An cinna wa motocin haya wuta a tashar Oyingbo da ke Legas

 


An cinna wa motocin haya wuta a tashar Oyingbo da ke Legas


Wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun sa wuta a tashar mota ta Oyingbo da ke cikin birnin Legas inda motoci da dama suka ƙone.

Yadda aka cinnawa tashar Oyingbo da ke Legas Wuta


Jaridar The Nation a Najeriya ta ruwaito cewa akwai aƙalla manyan motoci 20 a tashar motar a lokacin da aka sa wutar.


Haka zalika wani bidiyo da ke yawo a shafin Twitter ya nuna yadda manyan motocin ke kamawa da wuta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.