Jami’an tsaro sun kashe aƙalla Mutane 20 tare da jikkata fiye da 50 a zanga-Zangar EndSARS a Legas

 


Ƴan sanda sun buɗe wa dubban masu zanga-zanga wuta a Legas


Ana fargabar mutane da dama sun mutu bayan sojoji sun buɗe wa dubban masu zanga-zangar EndSars wuta a dandalin Lekki toll gate da ke birnin Legas a kudancin Najeriya da yammacin Talata.


Wani ganau ya ce Sai da aka bada umarnin akashe Nepa da kyamarorin tsaro Sannan aka budewa Masu Zanga-zanga wuta.


Masu zanga-zangar sun ci gaba da yin ta ne bayan da gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita ta sa’a 24 a jihar a ranar Talata da safe sakamakon ƙona wani ofishin yan sanda da aka yi.


BBC tana cikin nuna bidiyon ci gaban zanga-zangar kai tsaye a shafinta na Facebook a lokacin da aka fara harbe-harbe da bindiga a wajen.

Bidiyon yadda jami’an tsaro suka buɗewa Masu Zanga-zanga wuta a Legas


Dubban mutane ne suka sake taruwa a dandalin na Lekki toll gate suna ci gaba da zanga-zangar.


Amma nan da nan sai komai ya hargitse wajen ya cuɗe. Babu tabbas kan ko mutum nawa ne suka jikkata a lamarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 6:45pm na yamma.


Sannan babu bayanai a hukumance kan alkaluman mutane da suka mutu ko jikkata. Sai dai wani ganau ya tabbatar wa BBC cewa ya ƙidaya gawawwaki 20 an kuma jikkata sama da 50.


Tuni dai zanga-zangar ta rikiɗe zuwa rikici tsakanin masu yin ta da wasu da ake zargin ƴan daba ne a wasu manyan biranen Najeriya da suka haɗa da babban birnin tarayya Abuja.


Shi ma wakilin sashen BBC Pidgin ya ce ya ga mutum ɗaya da ya jikkata.


Rahotanni na nuna cewa ƴan sandan kwantar da tarzomar sun yi ƙawanya sun zagaye masu zanga-zangar da suka ƙi guduwa.


Kuma sauran waɗanda suka rage ba su gudu ɗin ba sun haƙiƙance cewa za su ci gaba da zanga-zangar EndSars ɗin.

 

Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya bayar da umarnin cewa ka da a fara aiki da dokar hana fitar sai ƙarfe 9 na daren Ranar takata saboda mutanen da cunkoson ababen hawa ya rutsa da su su samu damar koma wa gida.


Sojojin sun fara harba harsasai sama ne da farko, su kuma masu zanga-zangar suka fara amfani da abin wasan wuta don mayar wa sojojin martani, a cewar wakilin BBC Pidgin da ke wajen.

Bidiyon yadda jami’an tsaro suka buɗewa Masu Zanga-zanga wuta a Legas


Wasu masu zanga-zangar dai suna cewa mutane sun mutu ya yinda wasu suka jikkata bayan faruwar lamarin.


Leave a Reply

Your email address will not be published.