Buhari ya Yi wa ƴan Najeriya Jawabi game da zanga-Zangar EndSARS

 


Ga fassaran jawaban da Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a takaice game da halin da Nigeria ta tsinci kanta a yau:


1- Anyi ta’adi da barna sosai a zanga-zangar ENDSARS, an lalata kayan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu har da gidan babban basaraken jihar Lagos.


2- Nayi takaicin rasa rayuka da aka samu a dalilin wannan zanga-zanga.


3- An canza akalar zanga-zangar ta lumana zuwa wani abu dabam, wannan ba zamu lamunta ba dole za’ kare rayukan al’ummah da dukiyarsu.


4- Ba zamu taba yadda da cewa zanga-zangar luma ce ake yi ba, domin duniya ta ga irin barnar da akayi.


5- Labaran karya da ake ta yadawa a kafofin sada zumunta da kokarin kawar da gaskiya abin takaici ne.


6- Duniya ta shaida game da kokarin da mukeyi wajen tabbatar da gaskiya da adalci, a dena dogaro da labaran karya wanda yake fitowa daga gurin ‘yan adawa ko masu muguwar manufa ga Nigeria.


7- Wannan Gwamnati na kokarin kawo saukin rayuwa a cikin alummah.


8- Muna da babban tsari na fitar da miliyoyin ‘yan Nigeria daga kangin talauci da duniya ta fuskanta a dalilin annobar Coronavirus.


9- Mun ware kudi sama da naira bilyan 75 domin samar da aiki da sauki ga ‘yan kasa ba tare da bata lokaci ba, wannan na daga cikin kokarin da muke wajen samar da saukin rayuwa a Nigeria.


10- Babu wata gwamnatin Demokaradiyyah a Nigeria da take kokarin kawo sauyi da adalci kamar wannan gwamnatin.


11- Muna shirin tabbatar da sabon tsarin albashin ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro wanda zai biya bukatunsu bakin gwargwado.


12- Mun kawo sabon tsarin albashi ga Malaman makaranta.


13- Zamu cigaba da kawo tsari mai kyau a wannan gwamnatin.


14- Zamu tabbatar da cewa an kare ‘yan Nigeria da dukiyoyinsu a wannan yanayi da ake ciki.


15- A tuna gwamnati na da hakkin kare ‘yan kasa da dukiyarsu da daga kowani irin kalubale na ayyukan ta’addanci da tsageranci.


16- Zuwa gareku kasashen waje da kuka nuna damuwa a kan mu, muna godiya, amma ku dinga lura da labarun karya da ake yadawa game da halin zanga-zangar ENDSARS.


17- Ina rokon masu zanga-zanga da su lura da kokarin da muke wajen kawo sauyi a cikin kasa.


18- Kada ku biye wa miyagu su kawo cikas da barazanar tsaro da taka dokokin kasa, ba zamu taba barin haka ba.


19- Muna kira da a dakatar da zangar munji bukatunku, zamu biya.


20- Ku bar zanga-zanga, ku fita harkokinku na yau da kullum.


21- Hukumomin tsaro zasu tabbatar da tsaronku da dukiyarku ba tare da zalunci ba

22- Muna ta’ziyya wa rundinar ‘yan sanda da iyalansu wadanda aka kashe a dalilin wannan zanga-zangar.


23- Muna godiya ga gwamnonin Nigeria da shugabannin addinai da na gargajiya


24- Wannan gwamnatin na kokarin girmama kowa, amma ba zata taba barin wadanda zasu kawo matsala a kasa su ci nasara ba


25- Allah Ka albarkaci kasarmu Nigeria

Leave a Reply

Your email address will not be published.