Yadda rikicin zanga-zangar EnSars ya shafi Hausawa a kudancin Najeriya

 


Yadda rikicin zanga-zangar EnSars ya shafi Hausawa a kudancin Najeriya


Wasu da ake zargin masu zanga-zanga ne sun kashe mutum biyu tare da ƙona dukiyoyi a birnin Aba a Jihar Abia a jiya Laraba.


Lamarin ya faru ne yayin da mutanen ɗauke da adduna da katakwaye suka far ma wata kasuwar kayan gwari, wadda akasari Hausawa ne.


BBC ta tuntuɓi Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Abia, SP Geoffery Ogbonna, sai dai ya ce lokacin da aka kira shi lokacin barcinsa ne.


Gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita a biranen Aba da Umuhia, sai dai matakin bai sanyaya gwiwar masu zanga-zangar ba.


Alhaji Haladu Imam mai albasa na daga cikin shugabannin ‘yan arewa mazauna Aba kuma ya shaiada wa BBC cewa an far musu ne da misalin ƙarfe 4:30 na rana.


“Mun ji ƙarar harbin bindigogi kuma sojojin da ke wurin gaba ɗaya sun gudu,” in ji shi. “Sun ƙona ƙanana da manyan motoci kusan 30.”


A birnin Fatakwal ma an samu irin wannan hare-hare duk da dokar hana fita. Wani mazaunin yankin ya ce masu zanga-zangar na ƙone duk kayayyakin da suka tarar na Hausawa.

Yan bindiga sama da 100 sun kai hari Zamfara, sun hallaka mutane 20

https://www.arewagist.com.ng/2020/10/yan-bindiga-sama-da-100-sun-kai-hari.html?m=1

Leave a Reply

Your email address will not be published.